Da Dumi-Dumi: Wata Nakiya ta sake Fashewa a Hedkwatar Sojoji a Taraba

Da Dumi-Dumi: Wata Nakiya ta sake Fashewa a Hedkwatar Sojoji a Taraba

  • Wani abu ya sake fashewa karo na uku a baya bayan nan a jihar Taraba da ke arewa ta tsakiya a Najeriya
  • Sai dai wannan karon, bayanai sun nuna cewa fashewar ta auku ne a kusa da Hedkwatar sojoji amma babu wanda ya rasa rayuwarsa
  • Kakakin hukumar yan sanda na jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin, wanda ya auku da daren Talata

Taraba - Wani abun fashewa ya tashi a Hedkwatar Birged ta 6 ta rundunar sojin Najeriya dake Jalingo, babban birnin jihar Taraba, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Lamarin ya faru bayan dare ya yi nisa ranar Talata a bayan ginin sansanin amma ba bu wanda ya rasa ransa sanadin tashin nakiyar.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

A halin yanzun dakarun Soji sun hana bin duk wasu hanyoyi da zasu ɓulle zuwa Hedkwatar Sojojin domin dakile wani yunkurin da ka iya zama barazana ga rayuwar mutane.

Taswirar jihar Taraba.
Da Dumi-Dumi: Wata Nakiya ta sake Fashewa a Hedkwatar Sojoji a Taraba Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Babu wata sanarwa a hukumance daga kwamandan sansanin sojojin a halin yanzun da muke kawo wannan rahoton.

Wannan lamarin na ranar Talata ya shiga cikin jerin fashe-fashen bam da ake samu a jihar Taraba da ke yankin arewa ta tsakiya a Najeriya.

A watan Afrilu da ya gabata, an samu tashin wani abun fashewa da aka ɗana har guda biyu a tsakanin mako biyu a jihar ta Taraba.

Ɗaya daga cikin su wanda ƙungiyar ta'addanci da ke fafutukar kafa ƙasar Musulunci a Afirka ISWAP ta ɗauki nauyin dasa wa, ya yi ajalin mutum shida.

Kara karanta wannan

Cikakken Labari: Wani Bam Ya Tashi a Masallaci Yayin da Mutane ke tsaka da Sallar Jumu'a

Hukumar yan sanda ta tabbatar

Kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Taraba, DSP Usman Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce babu wanda ya rasa ransa sandin fashewar.

A rahoton Daily Trust, fashewar ta yi ƙara sosai a kusa da sansanin Sojin wanda ke kan hanyar Jolly Nyame, a birnin Jalingo.

Rahoton ya nuna cewa ƙarar Fashewar ta karaɗe kusan dukkan sassan Jalingo, amma bincike ya tabbatar da cewa babu wanda abun ya shafa.

Legit.ng Hausa ta tuntuɓi wani mazaunin anguwar da abun ya faru a Ibadan, Saidu Bobboji, ya ce sun ji ƙarar fashewar kuma mutane na tsammanin Gurneti ne ya fashe.

Bobboji ya shaida wa wakilin mu cewa lamarin na da ban tsoro amma inda Allah ya taimaka babu wanda ya ji rauni ko ya rasa rayuwarsa sanadin fashewar.

Ya ce:

"A halin yanzu, ba wanda ke bin hanyar wurin, an sanya tsaro mai tsanani. Abun ya zo da sauki kasancewar babu wanda ya shafa."

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

A cewar Bobboji, fashewar ta faru ne a cikin Barikin sojojin amma an hana mutane zuwa suga iya ɓarnar da abun ya yi.

A wani labarin kuma Wani Bam da yan ta'adda suka ɗana wa Sojoji ya koma kan su, ya musu mummunar ɓarna

Wani abun fashewa da yan ta'addan Boko Haram/ISWAP suka ɗana wa Sojojin Najeriya ya tashi da wata tawagar yan uwan su.

Bayanai sun nuna cewa yan ta'addan na kan hanyar dawowa daga kai farmakin sata lokacin da Nakiyar ta tashi da su, shida suka sheƙa barzahu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: