Da Duminsa: Tamkar ASUU, SSANU Da NASU Sun Gabatarwa FG Tsarin Biyan Albashi Da Suke So
- Kwamitin Hadin Gwiwa ta Kungiyar Ma’aikatan Ilimi Marasa Koyarwa da Makamantansu (NASU) da Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’o’in Najeriya (SSANU) ta gabatar wa da Gwamnatin Tarayya kafar da ta ke son a dinga biyansu
- Kafar da su ka gabatar ita ce University Peculiar Payroll Payment System (U3PS) ga Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu a Abuja ranar Talata
- Idan ba a manta ba, Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ma ta ki amincewa da kafar IPPIs wacce Gwamnatin Tarayya ta gabatar mata na biyan ma’aikata albashi inda ta kawo nata
Abuja - Kwamitin Hadin Gwiwa ta Kungiyar Manyan ma’aikatan jami’o’i (SSANU) da kuma Kungiyar Ma’aikatan Jami’o’i marasa koyarwa (NASU) ta gabatar wa Gwamnatin Tarayya kafar da ta ke so a dinga biyan ma’aikatanta albashi, Leadership ta ruwaito.
A ranar Talata kungiyar ta gabatar wa Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, kafar University Peculiar Payroll System (U3PS) a Abuja.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Dama tun farko kungiyoyin guda biyu kamar yadda Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), sun ki amincewa da kafar Integrated Payroll anda Personnel Information System (IPPIS), wacce Gwamnatin Tarayya ta gabatar musu don biyan ma’aikata albashi.
Yayin da ASUU ta zo da kafar University Transparency Accountability System (UTAS), JAC din SSANU da NASU ta kawo U3PS.
Saurari karin bayani ...
Asali: Legit.ng