Yan bindiga sun kashe mutum 8, sun gindaya sharuddan zaman lafiya a jihar Sokoto

Yan bindiga sun kashe mutum 8, sun gindaya sharuddan zaman lafiya a jihar Sokoto

  • Tsagerun yan bindiga sun sake kai hari kan mutanen gari a yankin ƙaramar hukumar Goronyo da ke jihar Sokoto
  • Mazauna ƙauyen sun yi kokarin tarbar maharan har suka kashe musu mutum uku, hakan ya fusata yan ta'addan suka kashe 8
  • A halin yanzun sun bukaci mazauna ƙauyen su tattara musu miliyan N10m na haraji idan suna son zaman lafiya

Sokoto - Wasu yan bindiga a jerin gwanon Mashina sun farmaki ƙauyen Taka Lime, da ke ƙaramar hukumar Goronyo a jihar Sokoto, inda suka kashe aƙalla mutum 8.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa maharan sun kuma tattara mutane da dama sun yi awon gaba da su, kuma sun sanar da mutanen kauyen abun da da zai sa su zauna lafiya.

Yan bindiga sun kara shiga Sokoto.
Yan bindiga sun kashe mutum 8, sun gindaya sharuddan zaman lafiya a jihar Sokoto Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Wani mazaunin ƙauyen Taka Lime wanda ya rasa matarsa da ɗiyarsa a harin, Sani Takakume, ya ce yan ta'addan sun shigo kuma suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.

Kara karanta wannan

Sokoto: Mutane sun mamaye tituna da zanga-zanga, sun nemi a saki waɗan da suka kashe ɗalibar da ta zagi Annabi

Ya ce:

"Mun fito da yawa ɗauke da dukkan wani nau'in makami domin mu kare kan mu daga maharan kuma muka ci nasarar kashe mutum uku, muka kama ɗaya."
"Da suka fahimci mutanen kauye sun kashe musu mayaƙa uku, sai suka kashe mutum 8 daga cikin yan uwan mu da suke tsare da su da nufin ɗaukar fansa."

Wane sharaɗi suka gindaya na zaman lafiya?

A cewarsa tuni yan bindigan suka bukaci a tattara musu zunzurutun kuɗi naira miliyan N10m a matsayin na fansar mutanen kauye da suka yi garkuwa da su.

Hakanan kuma sun gindaya sharaɗin cewa matukar mutane na son zaman lafiya a yankunan, dole su biya harajin miliyan N10m.

A wani labarin na daban kuma Daga ƙarshe, Gwamna Matawalle da Abdul-Aziz Yari sun kawo karshen rikicin APC a Zamfara

Kara karanta wannan

Cikakken Labari: Wani Bam Ya Tashi a Masallaci Yayin da Mutane ke tsaka da Sallar Jumu'a

Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, da tsohon gwamnan da ya gada, Abdul-aziz Yari sun gyara saɓanin dake tsakanin su.

Manyan jiga-jigan jam'iyya mai mulki sun garzaya wurin shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Adamu, sun shaida masa APC ta ɗinke a Zamfara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel