Rahoton gwamnati: Mutanen Legas kadai na cin naman shanu na N328bn a duk shekara

Rahoton gwamnati: Mutanen Legas kadai na cin naman shanu na N328bn a duk shekara

  • Rahoton da gwamnatin jihar Legas ta shaidawa masu labarai ya ce, akalla N328bn ake kashewa a sayen naman shanu a jihar
  • Wannan na zuwa ne daga bakin ma'aikatar harkar gona ta jihar a wani taron zuba hannun jari kan harkar abinci a jihar
  • Gwamnatin ta kuma bayyana shirinta na rage shigar da shanu jihar tare da inganta kiwon shanu na cikin gida nan da shekaru biyar

Jihar Legas - Rahoto daga gwamnati ya bayyana cewa, jihar Legas na cin naman saniya na kimanin Naira biliyan 328 a duk shekara.

Jaridar Premium Times ta ce, kimanin 98% cikin 100% na shanun da ake ci a jihar sun fito ne daga yankin Arewacin kasar ko kuma daga kan iyaka.

Kara karanta wannan

2023: PDP Ta Yi Watsi Da Batun Ba Wa Kudu Mulki, Ta Ce Kowa Na Iya Takarar Shugaban Ƙasa

Ragowar %2 cikin 100% na raguwar noman ana samar dashi ne a jihar kuma yana wakiltar kusan tan 181,757 na nama ko kuma kimanin shanu 1,235,601 a shekara.

Yadda mutan Legas ke cin naman shanu
Rahoto: Jihar Legas na cin naman sa na Naira biliyan 328 a duk shekara | Hoto: researchgate.net

Sakatariyar dindindin a Ma’aikatar Gona ta Jihar, Ibironke Emokpae ce ta sanar da hakan a ranar Litinin a Legas a wurin bikin tantance masu saka hannun jari 36 na kiwon shanu.

Ta kuma bayyana cewa, tantancewar ta zama dole domin harkallar shanun da ake yi a jihar Legas yana da matukar yawa.

Ta kara da cewa idan shirin sauya nama ya zo gaba daya zai taimaka wa gwamnatin jihar wajen kawar da tsadar kayayyaki na safarar shanu.

Misis Emokpae ta kuma jaddada cewa shirin samar da wuraren kiwon shanu zai cike gibin da ake samu da kuma samar da isasshen abinci da kuma dakile matsalar abinci a jihar.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Gwamnonin PDP sun shirya ganawar gaggawa gabanin zaben fidda gwani

A halin da ake ciki dai gwamnatin ta Legas na ta kokarin ganin yadda za ta shirya tsarin da zai kai ga rage shigo da shanu jihar, tare da inganta kiwonsu a cikin gida, kamar yadda Daily Nigerian ta tattaro.

Tashin hankali: Tsagerun Kudu sun kone mota makare da shanu da ta taso daga Arewa

A wani labarin na daban, wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan wata mota makare da shanu akan titin Ezinifitte/Uga a karamar hukumar Aguata ta jihar Anambra.

Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Lahadi, inji rahoton jaridar Punch.

A cewar wata majiya, motar tana kan hanyarta ta zuwa wata kasuwa a jihar ne, inda aka samu akasi ‘yan bindigar suka kai hari tare da kona ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel