Hanifa: Abdulmalik Tanko ya yarda da sace ta, ya karyata batun kashe yarinyar

Hanifa: Abdulmalik Tanko ya yarda da sace ta, ya karyata batun kashe yarinyar

  • Kotu dake sauraron karar makashin Hanifa, yar makaranta a Kano ta sake dage zaman zuwa ranar 10 ga watan Mayu
  • Sai dai a zaman na yau Litinin, Abdul Malik Tanko, ya yarda da sace marigayiyar amma ya ce bai san yadda aka yi ta mutu ba
  • Shugaban makarantar ya ce shi dai ya barta ne tana bacci a inda ya ajiye ta amma ko da ya dawo, sai ya tarar da ita a mace

Kano - Abdulmalik Tanko, malamin makaranta da ake zargi da sace dalibarsa mai shekaru 5, Hanifa Abubakar, da kuma ya kashe ta, ya sake musanta batun sanin yadda aka yi yarinyar ta mutu.

Ya karyata batun ne a babbar kotu mai lamba ta 5, da ke zama a Audu Bako a ranar Litinin, 9 ga watan Mayu, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Wani Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a APC Ya Sake Janye Takararsa

Hanifa: Abdulmalik Tanko ya yarda da sace ta, ya karyata batun kashe yarinyar
Hanifa: Abdulmalik Tanko ya yarda da sace ta, ya karyata batun kashe yarinyar Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Mai shari’a Usman Na’abba ne ya jagoranci zaman kotun.

Tanko, wanda a baya ya amince da hada baki da wasu wajen aikata laifin, ya musanta sauran tuhume-tuhume uku da ake masa da su da suka hada da yin garkuwa da yarinyar da kuma kashe ta daga baya.

Yayin da ya yarda cewa ya kai Hanifa makarantarsa sannan ya kulle ta, Tanko ya ce:

“Ba ni da tabbacin ko ni ne mutum na karshe da ya ganta a raye saboda tun da farko na sanar da wani batun. Ban kashe ta ba haka kuma ban bata guba ba. Na bar ta tana barci ne sannan na dawo na gan ta a mace.
“Ni da wadanda ake tuhuma na biyu da uku bamu san yadda aka yi ta mutu ba."

Kara karanta wannan

'Batanci: Atiku Ya Ce Ba Shine Ya Wallafa Rubutun Sukar Kashe Ɗalibar Sokoto a Shafinsa Ba

Idan za ku tuna, an sace Hanifa ne a ranar 4 ga watan Disamban 2021 a hanyarta ta komawa gida daga makarantar Islamiyya sannan daga bisani aka gano cewa an kashe ta.

Da farko Tanko ya tona cewa shine ya sace ta da kuma kashe ta bayan ya bata guba ta N100 kafin ya kuma binne ta a cikin wani rami a daya daga cikin makarantunsa.

An gurfanar da Abdulmalik tare da mutanen da ya hada kai da su, Hashim Isyaku da Fatima Bashir a gaban babbar kotun jihar Kano kan tuhume-tuhume biyar da suka hada da hada baki, garkuwa da mutum, daurewa, da kuma kisan kai wanda ya sabawa sashi na 97, 274, 277, 221 na doka.

An dage shari’ar zuwa ranar 10 ga watan Mayu domin ci gaba da sauraro.

Abin da wanda ya kashe yarinya ta ya fada mana da mu ka hadu - Mahaifiyar Hanifa a kotu

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Buhari Ya Roƙi ASUU Ta Janye Yajin Aiki, Ya Ba Wa Ɗalibai Haƙuri

A baya mun ji cewa Murja Suleiman Zubairu, wanda ita ce mahaifiyar Hanifa Abubakar ta bada labarin abin da ya faru tsakaninta da wanda ake zargi ya kashe mata ‘ya.

Daily Trust ta ce an gayyaci Murja Suleiman Zubairu a matsayin mutum na bakwai da ya gabatar da shaida a wannan shari’a da ake ta yi a kotu a jihar Kano.

Murja Zubairu mai shekara 38 a Duniya ta shaidawa Alkali yadda ta kai Marigayiya Hanifa makarantar Islamiyya a ranar Asabar, 4 ga watan Disamban 2021.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng