Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Sace Sarki Da Wasu Mutum 2 a Najeriya

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Sace Sarki Da Wasu Mutum 2 a Najeriya

  • Wasu yan bindiga kimanin su 20 sun afka garin Otuabula, karamar hukumar Ogbia a Jihar Bayelsa sun sace basarake da mutum biyu
  • Majiyoyi daga garin sun tabbatar da afkuwar lamarin inda suka ce misalin karfe 1 na dare maharan suka shigo kuma suka tsere da su a cikin jirgin ruwa
  • Bugu da kari, majiyoyin sun kuma ce maharan sun yi wa wani mazaunin garin rauni da wuka saboda ya gansu amma ya tsallake rijiya da baya

Bayelsa - Wasu yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace wani mai sarautar gargajiya, wani mutum dan shekara 50 da wani mai matsakaicin shekaru misalin karfe 1 na dare a Otuabula, karamar hukumar Ogbia a Jihar Bayelsa.

Nigerian Tribune ta rahoto cewa majiyoyi daga unguwar sun ce yan bindigan kimanin su 20 suka afka garin, suka sace babban basareken, Cif Otia Isomom, Mrs Lucy Osain da Mr Friday Abah suka tsere da su a cikin jirgin ruwa mai inji.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Sace Sarki Da Wasu Mutum 2 a Najeriya
'Yan Bindiga Sun Sace Basarke Da Wasu Mutum 2 a Bayelsa. Hoto: The Punch.
Asali: UGC

Majiyar daga garin ta kara sanar da Tribune Online cewa maharan sun yi wa wani mazaunin garin da ya gansu rauni da wuka amma ya tsallake rijiya da baya ba su kashe shi ba.

Yan sanda sun tabbaar da afkuwar harin

Mai magana da yawun yan sandan Jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, ya tabbatar da afkuwar lamarin kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Ya ce jami'ansu suna can sun dage suna kokarin ceto wadanda aka sace din, yayin da ake cigaba da bincike.

'Yan bindiga sun sace mutane 29 a wani ƙauyen Katsina, 'Yan Sanda

A wani rahoton, kun ji cewa mutane 29 ne yan bindiga suka sace yayin harin da suka kai kauyen Godiya a cewar rundunar yan sandan Jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Wani Bam ya ƙara tashi mutane na tsaka da holewa a jihar Kogi, rayuka sun salwanta

Mai magana da yawun rundunar a jihar, Gambo Isah, ya tabbatar da adadin mutanen yayin zantawa da Channels Television a ranar Talata.

Wasu gungun yan bindiga ne suka kai hari a Ruwan-Godiya a daren ranar Lahadi a karamar hukumar Faskari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel