Fusatattun fasinjoji sun toshe filin jirgin Abuja saboda jinkirin tashin jirgi
- Wasu fusatattun fasinjoji sun tare kofar shiga filin jirgin Nnamdi Azikiwe da ke Abuja saboda jinkirin tashin jirgi
- Fasinjojin sun kasance a filin jirgin ne tun a daren ranar Lahadi don shiga jiragensu zuwa wurare daban-daban
- Sai dai har zuwa safiyar yau Litinin suna nan kara zube ba tare da wani kwakkwaran bayani daga ma'aikatan jirgin ba, lamarin da ya tunzura su
Abuja - Fusatattun fasinjoji masu yawan gaske sun tare kofar shiga filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja sakamakon tsaikon da aka samu a wajen tashinsu.
Fasinjojin wadanda suka fusata a safiyar ranar Litinin, 9 ga watan Mayu, sun bayyana cewa sun kasance a filin jirgin tun a daren ranar Lahadi domin tashi zuwa wurare mabanbanta.
Da misalin karfe 8:36 na safe, fasinjojin kamfanin jirgi na Arik wanda ya kamata su tashi da misalin karfe 7:00 na yammacin ranar Lahadi na nan a wajen zaman matafiya ba tare da wani bayani daga ma’aikata ko jami’an jirgin ba.
Wani fasinja ya samar da jaridar Premium Times cewa:
“Sun rigada sun jinkirta shi daga karfe 7 zuwa 9 na daren jiya. Daga 9:45 na jiya har zuwa yanzu.”
Jaridar The Cable ta rahoto cewa fasinjoji sun kwana cike da takaici a filin jirgin yayin da kujerun wajen ne suka zame masu gadajen kwanciya.
Kamfanonin jiragen sama sun hakura, sun fasa tafiya yajin aiki
A gefe guda, mun ji a baya cewa kamfanonin jiragen sama na Najeriya sun dakatar da hukuncinsu na gurgunta bangaren sufurin jiragen sama na Najeriya ta hanyar tafiya yajin aiki a ranar Litinin.
Daily Trust ta ruwaito cewa, shugaban AON, Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina, wanda ya sanar da hakan a ranar Lahadi, ya ce wannan hukuncin ya biyo baya ne bayan tattaunawa da suka yi da gwamnatin tarayya.
Wannan cigaban ya zo ne bayan a kalla kamfanonin jiragen sama shida sun zare kansu daga yunkurin tafiya yajin aikin a fadin kasar nan.
Asali: Legit.ng