Da duminsa: Kamfanonin jiragen sama sun hakura, sun fasa tafiya yajin aiki

Da duminsa: Kamfanonin jiragen sama sun hakura, sun fasa tafiya yajin aiki

  • Kungiyar kamfanonin jiragen sama ta Najeriya, AON, ta sanar da hukuncinta na fasa yajin aikin da ta yi niyyar fadawa a ranar Litinin
  • Da farko kungiyar ta sha alwashin gurgunta bangaren sufurin jiragen sama na Najeriya ta hanyar shiga yajin aiki saboda tsadar man jirgin saman
  • Alhaji Abdumunaf Yunusa Sarina, shugaban kungiyar AON ya sanar da hukuncinsu a ranar Lahadi duk da tashin gwauron zabin da farashin mai ya yi

Kamfanonin jiragen sama na Najeriya sun dakatar da hukuncinsu na gurgunta bangaren sufurin jiragen sama na Najeriya ta hanyar tafiya yajin aiki a ranar Litinin.

Daily Trust ta ruwaito cewa, shugaban AON, Alhaji Abdulmunaf Yunusa Sarina, wanda ya sanar da hakan a ranar Lahadi, ya ce wannan hukuncin ya biyo baya ne bayan tattaunawa da suka yi da gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Hadimin Buhari, Bashir Ahmad ya yi murabus daga kujerarsa

Da duminsa: Kamfanonin jiragen sama sun hakura, sun fasa tafiya yajin aiki
Da duminsa: Kamfanonin jiragen sama sun hakura, sun fasa tafiya yajin aiki
Asali: Original

Wannan cigaban ya zo ne bayan a kalla kamfanonin jiragen sama shida sun zare kansu daga yunkurin tafiya yajin aikin a fadin kasar nan.

Kamfanonin jiragen saman da tun farko suka janye daga shiga yajin aikin kan tashin gwauron zabin da farashin man jirgin sama yayi a kasar nan, sun hada da Ibom Air, Dana, Arik, Aero, Overland da Green Africa Airways.

Daga cikin shidan da suka janye tun farko, kamfanin Green Africa ne kadai ba ya cikin kungiyar AON.

Karin bayani na tafe...

Asali: Legit.ng

Online view pixel