Afuwar da Shugaba Buhari ya yi wa tsofaffin barayin kasa ta jawo an maka shi gaban kotu
- Socio-Economic Rights and Accountability Project ta na karar gwamnatin Muhammadu Buhari a kotu
- Kungiyar za tayi shari’a da Muhammadu Buhari saboda ya yafewa wasu wadanda aka samu da laifi
- SERAP ta na kalubalantar Gwamnatin Tarayya a kan yi wa Joshua Dariye da Jolly Nyame afuwa
Lagos - Kungiyar Socio-Economic Rights and Accountability Project wanda aka fi sani da SERAP ta shigar da kara a kotu a kan Mai girma Muhammadu Buhari.
Jaridar Punch a wani rahoto da ta fitar a ranar Lahadi, 9 ga watan Mayu 2022, ta ce SERAP ta na kalubalantar afuwar da shugaban Najeriyan ya yi wa masu laifi.
Mataimakin Darektan wannan kungiya mai zaman kan ta, Kolawole Oluwadare ya fitar da wani jawabi na musamman, inda ya bayyana matsayar da suka dauka.
Mista Kolawole Oluwadare ya ce sun kai shugaban kasa kotu ne saboda yafewa Sanata Joshua Dariye da Jolly Nyame laifin da suka aikata na satar kudin jama’a.
An shigar da kara a Legas
A karar da SERAP ta shigar mai lamba FHC/L/CS/825/2022 a babban kotun tarayya da ke Legas, ta nemi Alkali ya yi bayanin ko shugaban kasa yana da wannan iko.
Kungiyar ta na so kotu ta raba gardamar cewa afuwar da gwamnatin tarayya ta yi wa Dariye da Nyame bai ci karo da rantsuwar da shugaban Najeriyan ya yi ba.
PM News ta ce SERAP ta na ikirarin yafewa tsofaffin gwamnonin ya ci karo da abin da al’umma su ke so, sannan ya sabawa yakin da ake neman yi da rashin gaskiya.
Inda matsalar ta ke - SERAP
A cewar lauyoyin kungiyar, idan ba a janye wannan afuwa ba, za a samu karuwar marasa gaskiya a Najeriya, sannan a rika yafewa ‘yan siyasan da suka aika laifuffuka.
Rahoton ya ce SERAP ta ce idan za a yafewa wadanda aka samu da aikata laifi, bai dace a katange ‘yan siyasan da suka ci amana, suka wawuri dukiyar talakawansu ba.
A karshe kungiyar ta na so nan gaba a rika la’akari da yaki da rashin gaskiya wajen yafewa masu laifi. Abubakar Malami yana cikin wadanda za su kare kansu a kotu.
Har zuwa yanzu ba a sa ranar da Alkali zai saurari wannan kara domin a yanke hukunci ba.
Nyame da Dariye sun sha
A 2018 kotu ta daure Jolly Nyame da Joshua Dariye a gidan yari bayan samun su da laifin satar N1.16b da N1.6bn daga cikin baitul-malin jihohin Taraba da kuma Filato.
Kwanakin baya aka ji labari gwamnati ta yafe masu da wasu mutane su 159 da ke tsare a kurkuku. Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin yafewa masu laifin.
Asali: Legit.ng