Da dumi-dumi: Kotu ta ragewa tsohon gwamna Dariye wa'adin zaman gidan yari
Kotun daukaka kara da ke babban birnin tarayya Abuja da rage wa'adin zaman gidan yari da aka yankewa tsohon gwamnan jihar Plateau, Joshua Dariye.
Kotun ta rage wa'adin daga shekaru 14 zuwa shekaru 10.
DUBA WANNAN: Shari'ar Maryam Sanda: Shedu sun fadawa kotu yadda aka kashe Bilyaminu
An dai yankewa Dariye hukuncin ne bayan samunsa da laifin almundaha da almubazarranci da dukiyar al'ummar jihar Plateau a yayin da yake gwamna a jihar karkashin jam'iyyar PDP.
A dai watan Yuni ne babban kotun gwamnatin tarayya da ke zamanta a Gudu a Abuja ta yankewa Dariye hukuncin zaman shekaru 14 a gidan kurkuku.
Sai dai kotun daukaka karar ta ce kotun ta yi kuskure a yayin da ta yankewa Dariye hukuncin shekaru 14 tunda wannan shine karo na farko da kotu ta same shi da aikata laifi.
A cewar kotun, dokar hukunta masu aikata laifuka bai bayar da damar a yankewa mai aikata laifi na farko wa'addin da ya kai shekaru 14 ba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng