Hotuna: Tinubu, Amaechi Da Shettima Sun Halarci Naɗin Sarautar Ƙanin Aisha Buhari

Hotuna: Tinubu, Amaechi Da Shettima Sun Halarci Naɗin Sarautar Ƙanin Aisha Buhari

  • Mai martaba Lamidon Adamawa, Dr Muhammadu Barkindo Aliyu Mustapha ya yi wa kanin Aisha Buhari sarauta a masarautar Adamawa.
  • Manyan mutane daga sassan Najeriya daban-daban sun hallarci taron nadin ciki har da Bola Tinubu, Rotimi Amaechi da Kashim Shettima
  • Al'umman gari ma ba a basu a baya ba domin fadar ta Lamidon Adamawa ta cika da masoya da masu fatan alheri ga Mahmud Halilu Ahmad aka Modi

Yola, Adamawa - An yi wa kanin Aisha Buhari, Mahmud Halilu Ahmad da aka fi sani da Modi nadin sarautar gargajiya a masarautar Adamawa, rahoton Daily Trust.

Lamidon Adamawa, Dr Muhammadu Barkindo Aliyu Mustapha ne ya nada sarautar ga surukin na Buhari a bikin da manyan mutane da dama suka halarta.

Asiwaju Bola Tinubu, jagoran jam'iyyar APC na kasa, Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi da Sanata Kashim Shettima suna cikin manyan mutane da suka hallarci taron.

Kara karanta wannan

'Batanci: Bayan Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Deborah a Sokoto, Osinbajo Ya Yi Magana Da Kakkausar Murya

Ga wasu daga cikin hotunan taron kamar yadda Daily Trust ta rahoto:

Hotuna: Tinubu, Amaechi Da Shettima Sun Halarci Naɗin Sarautar Ƙanin Aisha Buhari
Nadin Sarautar Kanin Aisha Buhari a Adamawa. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Hotuna: Tinubu, Amaechi Da Shettima Sun Halarci Naɗin Sarautar Ƙanin Aisha Buhari
Hotunan Tinubu, Amaechi Da Shettima Sun Halarci Naɗin Sarautar Modi. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Hotuna: Tinubu, Amaechi Da Shettima Sun Halarci Naɗin Sarautar Ƙanin Aisha Buhari
Tinubu da Shettima yayin da suka iso nadin sarautar kanin Aisha Buhari. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Hotuna: Tinubu, Amaechi Da Shettima Sun Halarci Naɗin Sarautar Ƙanin Aisha Buhari
Amaechi Da Shettima Wurin Naɗin Sarautar Ƙanin Aisha Buhari. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Hotuna: Tinubu, Amaechi Da Shettima Sun Halarci Naɗin Sarautar Ƙanin Aisha Buhari
Dandazon al'umma da suka hallarci nadin sarautar Modi. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Sarkin Daura: Mun ba Yusuf Buhari sarauta ne don kada ya riƙa gararamba a Abuja bayan Buhari ya sauka mulki

A wani labarin, Mai martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouk, ya yi magana kan dalili da yasa aka nada Yusuf, dan Shugaba Muhammadu Buhari sarauta a Daura, rahoton Daily Trust.

Yusuf, wanda shine da namiji tilo na Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Asabar, aka nada shi sarautar Talban Daura kuma Hakimin Kwasarawa.

Da ya ke jawabi a fadarsa yayin bikin nadin sarautar sabbin hakimai hudu, a ranar Alhamis, sarkin ya ce nadin zai hana Talban yawo zuwa Abuja da Yola, garin mahaifiyarsa, bayan wa'adin mulkin Buhari ta kare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel