Ban yanke shawarar yin takara ba, amma nan da yan kwanaki: Gwamnan CBN
- Godwin Emefiele ya yi fashin baki kan lamarin takararsa kujerar shugaban kasa a zaben 2023
- Emefiel ya bayyana cewa idan har yana son takara kujerar, da kudin da ya tara zai biya milyan dari
- Jam'iyyar PDP, Gwamnan jihar Ondo, da wasu yan Najeriya sunce Emefiel yayi murabus daga kujerarsa
Gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele, ya yi magana karon farko kan maganar sayan Fam na takara kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar All Progressives Congress APC.
Gwamnan ya ce ban yanke shawara kan yin takara kujerar shugaban kasa ba.
Emefiele, a jawabin da ya saki ranar Asabar, a shafinsa na Tuwita ya ce a yanzu dai zai cigaba da aiki karkashin mulkin shugaba Muhammadu Buhari amma nan da yan kwanakin zai yanke shawara.
Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa Buhari ba zai binciki wadanda ke siyan fom din miliyan N100 ba
A cewarsa, ko da zai yi takara da guminsa zai sayi Fam din naira milyan 100 ba sai manoma sun tara masa ba.
Yace:
"Ban yanke shawara ba. Amma ina godewa manoma da masoyan da suka tara min kudi don sayan Fam din takara shgaban kasa. Amma idan zan amsa kiransu, da kudin aikin banki na shekaru 35 da nayi ina aiki zan sayi Fam da kai na.
"Ba sai na bi ta bayan fagge ba kuma bisa dokoki da kundin tsarin mulki."
"Zan cigaba da aiki wa yan Najeriya karkashin mulkun shugaba Muhammadu Buhar. Zan yanke shawara tare da shiriyar Allah nan da yan kwanaki."
2023: Gwamnan APC ya ba Buhari shawarar tsige Gwamnan CBN idan bai janye takara ba
Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu ya fadawa shugaban kasa ya tsige Godwin Emefiele idan ya cigaba da neman shugabancin Najeriya.
Jaridar Daily Trust ta ce Gwamna Oluwarotimi Akeredolu ya yi wannan kira ne jim kadan bayan gwamnan na CBN ya yanki fam din tsayawa takara a APC.
Godwin Emefiele ya saye fam din neman shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC mai mulki, a lokacin da ya ke rike da shugabancin babban bankin kasa.
Asali: Legit.ng