N100m: Za mu binciki kudaden da aka yi amfani wajen sayan Fom din takara, Shugaban EFCC

N100m: Za mu binciki kudaden da aka yi amfani wajen sayan Fom din takara, Shugaban EFCC

  • Shugaban hukumar EFCC ya bayyana cewa za'a binciki yan siyasan dake sayen Fam din takara kujeran shugaban kasa
  • Yan Najeriya tuni sun yi Alla-wadai da farashin da jam'iyyun siyasa suka sanyawa tikitin takara
  • Jamm'iyyar All Progressives Congress (APC) take sayar da Fom din shugaban kasa N100m, ita kuma jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) na sayar da na ta N40m

Abuja - Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC ta bayyana cewa za ta tabbatar da cewa kudaden da akayi amfani wajen sayan Fom na takaran zaben na Halal ne.

Shugaban hukumar, AbdulRashid Bawa, a ranar Juma'a ya bayyana hakan yayin hirarsa a shirin Politics Today na gidan talabijin Channels.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Hadimin Buhari, Bashir Ahmad ya yi murabus daga kujerarsa

A cewarsa, wannan hurumin hukumar zabe INEC ne amma duk da haka zasu bibiyi kudaden don sanin asalin inda kudaden suka fito.

Yace:

"Kan lamarin bibiyan kudaden zabe da yan takara, wannan aikin INEC ne amma muna aiki tare da INEC da sauran hukumomi don tabbatar da cewa mun san inda kudin ya fito, na Halal ne ko Haram."

Shugaban EFCC
N100m: Za mu binciki kudaden da aka yi amfani wajen sayan Fom din takara, Shugaban EFCC Hoto: Aso Rock Villa
Asali: Facebook

Jawabin Bawa ya biyo bayan koke-koken da yan Najeriya ke yi bisa farashin Fom din takara da jam'iyyun siyasan Najeriya suka sanya.

Yayinda jam'iyyar All Progressives Congress (APC) take sayar da Fom din shugaban kasa N100m, jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) na sayar da na ta N40m.

Masu sharhi kan lamuran yau da kullum sun bayyana cewa wannan abu na da illa ga demokradiyyar Najeriya saboda sai mai kudi zai iya takara.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: PDP ta fallasa 'dabarar' da ta sa Jam’iyyar APC ta saida fam a kan N100m

'Yar takara mai shekara 102: EFCC, ICPC su kama duk dan takarar da ya siya fom N100m

A wani labarin kuwa, an tura sako ga hukumar yaki da rashawa, EFCC da hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta, ICPC da su yi ram da duk dan takarar da ya siya fom kan kudi N100 miliyan.

Tsohuwa mai shekaru 102, 'yar takarar kujerar shugaban kasa a shekarar 2023, Mrs Josephine Ezeanyaeche ce ta tura sakon.

Kai tsaye, tana bukatar jami'an tsaro su damko gami da gurfanar da duk wani 'dan siyasa ko kungiyar da ta siya fom din takara N100 miliyan na duk wata jam'iyyar siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng