Abinda ya kamata ka sani game da mutum 23 da suka sayi Fom din APC N100m kawo yau (Hotuna)
Adadin masu neman takarar kujeran shugaban kasa karkashin jam'iyyar All Progressives Congress APC na kara yawaita duk da tsadar farashin kudin Fam din jam'iyyar.
Jama'ar Najeriya, musamman masu sharhi kan lamuran yau da kullum sun yi tsokaci kan farashin kudin.
Kawo yanzu, kimanin mutum 20 ne suka ayyana niyyar takara karkashin APC amma yan kalilan suka sayi Fam din.
Ga jerin wadanda suka yankin Fam na N100m kawo yanzu:
1. Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Tsohon gwamnan jihar Legas (1999-2007)
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
2. Yahaya Adoza Bello
Gwamnan jihar Kogi (2016 - yanzu)
3. Dave Umahi
Kano: Shugaban Ma'aikatan Fadar Ganduje, Shugaban Karamar Hukuma, Ƴan Majalisa 2, Auditan APC Da Shugaban Matasa Duk Sun Koma NNPP
Gwamnan jihar Ebonyi (2015- yanzu)
4. Emeka Nwajiuba
Karamin Ministan Ilimi (2019 kawo yanzu)
5. Chibuike R. Amaechi
Kakakin majalisar dokokin jihar Rivers (1999-2007), Tsohon gwamnan jihar Rivers (2007-2015), Ministan Sufuri (2015-kawo yanzu).
6. Fasto Nicholas Felix
Fasto mazauni kasar Amurka
7. Farfesa Yemi Osinbajo
Tsohon Fasto kuma Mataimakin shugaban kasa (2015- kawo yanzu)
8. Ken Nnamani
Tsohon Shugaban majalisar dattawan Najeriya
9. Fasto Tunde Bakare
Tsohon abokin takaran Shugaban Buhari a 2011 kuma Faston Latter Rain Assembly
10. Dimeji Bankole
Tsohon kakakin majalisar wakilan tarayya (2007-2011)
11. Rochas Okorocha
Tsohon gwamnan jihar Imo (2011-2019)
12. Ibikunle Amosun
Tsohon gwamnan jihar Ogun (2011-2019)
13. Sanata Robert Ajayi Boroffice
Sanata mai wakiltar Ondo ta Arewa (2011 - yanzu)
14. Ogbonnaya Onu
Ministan Kimiya da fasaha (2015 - yanzu)
15. Benedict Ayade
Gwamnan jihar Cross Rivers (2015-yanzu)
16. Timipre Sylva
Tsohon gwamnan jihar Bayelsa (2007-2011), Ministan Man Fetur (2019-yanzu)
17. Ahmad Ibrahim Lawan
Tsohon dan majalisan wakilai (1999–2007), Dan majalisan dattawa (2007-yanzu), Shugaban majalisar dattawa (2019-yanzu)
18. Ken Nnamani
Dan majalisar dattawa (2003-2007), Shugaban majalisar dattawa (2005-2007)
19. John Kayode Fayemi
Gwamnan jihar Ekiti (2010-2014), Ministan ma'adinai (2015-2018), Gwamnan jihar Ekiti karo na biyu (2018-yanzu).
20. Mrs. Uju Kennedy
21. Chris Ngige
Gwamnan jihar Anambra (2003–2006), Ministan kwadago (2015-yanzu)
22. Abubakar Badaru Talamiz
Gwamnan jihar Jigawa (2015-yanzu)
23. Godwin Emefiele
Tsohon Manajan Zenith Bank, Gwamnan bankin tarayya CBN (2014-yanzu)
Asali: Legit.ng