Babban Kotu Ta Tuɓe Wa Wani Basarake Rawaninsa a Najeriya

Babban Kotu Ta Tuɓe Wa Wani Basarake Rawaninsa a Najeriya

  • Wata babbar kotun Jihar Anambra da ke zama a Ogidi ta tsige wani basaraken garin Alor a karamar hukumar Idemili ta kudu cikin jihar, Igwe Mac Anthony Okonkwo
  • Hakan ya biyo bayan karar da wani Chief Uzoma Igbonwa ya yi, ta lauyansa, Bona Oraekwe yana kalubalantar cancantar Okonkwo a mukamin tun 2014 da gwamnati ta nada shi
  • Yayin da alkali Pete Obiorah ya yanke hukunci, ya bukaci Okonkwo da ya guji zuwa fada ko kuma amfani da fadar Obi Eze Angbudugbu, wacce ita ce asalin fadar da mutanen Alor su ka gada tun kakanni

Anambra - Wata babbar kotun Jihar Anambra ta tube rawanin basaraken garin Alor da ke karkashin karamar hukumar Idemili ta kudu a cikin Jihar Anambra, Igwe Mac Anthony Okonkwo, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Lauya ya kwashe kudin dake akawunt din dan sanda bayan ya mutu, EFCC ta damkeshi

Umarnin ya biyo bayan wata kara da Chief Uzoma Igbonwa ya maka shi ta lauyansa, Bona Oraekwe, inda ya kalubalanci cancantar Okonkwo na zama shugaban yankin Alor (Ezedioramma III) tun shekarar 2014 da gwamnatin jihar ta nada shi.

Babban Kotu Ta Tuɓe Wa Wani Basarake Rawaninsa a Najeriya
Kotu Ta Tuɓe Wa Wani Basarake Rawaninsa a Anambra. Hoto: Daily Trust.
Asali: UGC

Okonkwo da wasu mutane biyu, Frank Nwabufo Okoye da Ifenna Okafor sun kai kara mai lamba: HID/354/2019 inda su ka kalubalanci amintattun da aka sanya na Majalisar Mutanen Alor (APA) da Igbonwa kuma sun bukaci APA din da aka yi wa rijista karkashin bangare na uku na Dokar Kamfanoni da Batutuwa masu Kama da hakan (CAMA) na 1990, cewa ba kungiyar da gwamnati ta kafa a garin ba ce, don haka bai dace ta dinga aiwatar wa Gangamin Mutanen Alor (APC) aiki ba, wacce kungiya ce sananna da gwamnati ta kafa wa mutanen Alor.

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

Sun bukaci kotu ta rushe APA ta koma APC

The Guardian ta ruwaito yadda a cikin takardar su ka bukaci kotu ta rushe sauyin sunan APC zuwa APA da wanda su ke kara ya yi a Hukumar Harkokin Kamfanoni (CAC).

Sannan sun bukaci kotu ta dakatar da APA daga aikin APC tare da yin taron ko wacce shekara da Majalisar Alor ta ke yi wanda ya ke kunsar duk wasu manyan maza da mata da ke garin Alor.

Yayin da alkali, Pete Obiorah ya yi hukunci, ya umarci Okonkwo da ya kiyaye zuwa fada ko kuma amfani da fadar Obi Eze Agbudugbu (asalin fadar da mutanen Alor su ka gada daga kakanni).

Alkalin ya bukaci a fara shirye-shiryen nadin sabon basaraken da zai maye gurbin Okonkwo

Sannan ya nada Igbonwo a matsayin zababben shugaban APC kamar yadda hukuncin da kotu ta yi a ranar 5 ga watan Fabrairun 2019 ya nuna, sannan Yankin Gundumar Alor ta fara kokarin zaben wanda zai maye gurbin kujerar Igwe na Alor kamar yadda kundin tsarin mulkin APC na 2011 ya tanadar.

Kara karanta wannan

Kano: Tsohon Kwamishinan Ganduje Ya Fita Daga Jam'iyyar APC

A cewar alkalin:

“Na bayyana zabe da kuma nadin Okonkwo a matsayin shugaban gargajiyan garin Alor da kwamitin rikon kwaryar APC ta yi tsakanin ranar 7 ga watan Afirilu da 17 ga watan Mayun 2014 a matsayin rusasshe kuma ya ci karo da kundin tsarin mulkin APC ta 2011 wanda ya maye gurbin kundin tsarin mulkin APC na 1992 da kuma dokar shugabannin gargajiyar Jihar Anambra na 2007 da kuma ko wacce dokar da ta shafi shugabannin gargajiya.”

Gwamna ya kori surukinsa daga aiki, ya umurci kwamishina ya maye gurbinsa

A wani rahoton, Gwamnan Jihar Abia, Okezie Ikpeazu, ya sanar da korar surukinsa, Mataimakin Manajan, Hukumar Kare Muhalli ta JIhar Abia, ASEPA, ta Aba, Rowland Nwakanma, a ranar Alhamis, The Punch ta ruwaito.

A cikin wata takarda da sakataren gwamnatin jihar Abia, Barista Chris Ezem ya fitar, Ikpeazu ya kuma 'sallami dukkan shugabannin hukumar tsaftace muhalli a Aba amma banda na Aba-Owerri Road, Ikot Ekpene da Express.'

Kara karanta wannan

Sokoto: Bishop Kukah ya yi martani kan kashe dalibar da ta yi batanci ga Annabi

Amma gwamnan ya bada umurnin cewa dukkan 'masu shara ba a kore su ba, su cigaba da aikinsu na tsaftacce hanyoyi da tituna a kowanne rana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164