An kammala gyaran layin dogon Abuja- Kaduna, an sanar da lokacin dawowar karakainar jirage

An kammala gyaran layin dogon Abuja- Kaduna, an sanar da lokacin dawowar karakainar jirage

  • A ranar Alhamis, kamfanin sufurin jirgin kasan Najeriya ya ce an kammala gyaran wuraren da 'yan ta'adda suka barnata yayin kai harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna
  • Mummunan lamarin ya auku a ranar 28 ga watan Maris, 2022, wanda ya yi sanadiyyar lashe rayukan mutane 9, raunata wasu, gami da garkuwa da mutane da dama
  • Kamfanin bai yi magana a kan halin da wadanda aka yi garkuwan dasu ke ciki ba, amma a sanarwa da ya bayar a baya, ya ce an gyara layikan jirgin kasan ba tare da jinkiri ba, gami da tsananta tsaro don tabbatar da lafiyar fasinjoji

Abuja - A ranar Alhamis kamfanin sufurin jirgin kasan Najeriya (NRC), ya ce an kammala gyaran wuraren da 'yan ta'addan suka barnata yayin kai harin jirgin kasan da ya taso daga Abuja zuwa Kaduna a ranar 28 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

Harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane tara, bayan garkuwan da aka yi da mutane da dama, wadanda suka hada da wata tsohuwa, wata mata mai goyo, da dai sauransu.

An kammala gyaran layin dogon Abuja- Kaduna, an sanar da lokacin dawowar karakainar jirage
An kammala gyaran layin dogon Abuja- Kaduna, an sanar da lokacin dawowar karakainar jirage. Hoto daga vanguardngr.com
Asali: Twitter

A wata takarda da aka bayyanawa manema labarai, NRC ta ce an yi gyaran hanya tsakanin biranen biyu, duk da ta gaza samar da bayani game da mutane 141 da har yanzu suna hannun masu garkuwa da mutane, Vanguard ta ruwaito.

A takardar da Niyi Alli yasa hannu a maadadin manajan daraktan kamfanin, Fidet Okhiria, ya nuna:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"An gyara hanyoyin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna. Hakan na nuna cewa an gyara manyan hanyoyin jirgin kasan."

Daily Trust ta ruwaito cewa, an hada kudancin karshen jirgin, wanda abunda aka dasa mai fashewa ya lalata da arewancin karshen gefen. Yanzu an gyara hanyar jiragen Kaduna da na Abuja.

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

"Loco 2502 ne jirgin da hatsarin ya auku (duk da ba a barnatashi ba), inda aka tare jirgin a karshen Rigasa, a halin yanzu an kai shi karshen Idu, gami da mika shi wurin gyara don a duba shi tare da kula da shi yadda ya dace.
"Kamar yadda muka ambata a baya, jirgin Abuja zuwa Kaduna zai dawo kan aiki ba da jimawa ba tare da karin tsananta tsari,' a cewarsa.
"Ana bukatar fasinjoji su gabatar da katin dan kasarsu lokacin tantancewa kafin siyan tiketi. Hakan za a dinga don samun cikkaken bayani akan fasinjoji da kuma tsare rayuwarsu yayin tafiya.
"Kamfanin na maida hankali wajen tabbatar ta tsare rayuwar dukkan fasinjojinmu da ma'aikata yayin tafiya. Zamu cigaba da hada kai da jami'an tsaro don tabbatar an ceto duk wanda aka yi garkuwa dashi ba tare da wani rauni ba, gami da sada shi da iyalinsa nan kusa.

Kara karanta wannan

Iftila'i: An tafka ruwan sama a Damaturu, ya rusa gidaje, ya hallaka mutane 5

"Za mu cigaba da addu'a daga wadanda suka rasa rayukansu a harin jirgin. Har ila yau, muna rokon Ubangiji da ya cigaba da ba wa iyalan wadanda suka rasa masoyansu hakurin jure rashin da suka yi. Sannan muna wa wadanda suka samu raunuka a jirgin kasan AK9 a ranar 28 ga watan Maris, 2022 fatan warkewa cikin gaggawa.
"Tare da bin umarnin shugaban kasa, muna karfafa duk wanda har yanzu yake neman masoyinsa ko neman wani karin bayani da ya tuntubemu ta wadannan lambobin: Mrs. Lola 080233101145 da Mr Mahmood 07038356015
"NRC na cigaba da bayyana godiyarta ga hukumomin tsaro saboda goyan bayan da suka cigaba da badawa, musamman don ganin sun tsare mana ma'aikata da jami'ai a wurin da lamarin ya auku.
"Kamar kullum, kamfanin zai cigaba da sanarwa al'umma sabbin cigaban idan an samu." takardar ta kara da cewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng