Jami'in hukumar LASTMA ya yanke jiki ya faɗi matacce yana tsaka da aiki
- Wani jami'in hukumar rage cunkoso ta jihar Legas, LASTMA, ya rasa rayuwarsa yayin da yake tsaka da aiki a Ojota Post, Legas
- Bayanai sun nuna cewa Jami'in mai ba da hannu ya yanke jiki ya faɗi ya rasu nan take duk da mutane sun kawo masa ɗauki
- Babu wani cikakken bayani kan musabbabin mutuwarsa, amma dai an ɗauke gawarsa zuwa ɗakin aje gawarwaki na Asibiti
Lagos - Mutane sun ga tashin hankali da sanyin safiyar ranar Alhamis, lokacin da wani Jami'in hukumar rage cunkoso ta jihar Legas, LASTMA, ya yanke jiki ya faɗi.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa Jami'in ya faɗi ba zato ba tsammani yayin da yake tsaka da gudanar da aikinsa kuma Allah ya masa rasuwa nan take a Ojota Post, jahar Legas.
A cewar wani shaida da abun ya faru a idonsa, Mista Ibrahim Ajao, lamarin mai ta da hankali ya auku ne da mislin ƙarfe 7:30 na safe lokacin mutane na kokarin wucewa.
Ya ce faɗuwar jami'in mai ba da hannu ya jawo hankulan masu wucewa da masu jajantawa waɗan da suka yi yunkurin ceto rayuwarsa, amma taimakon farkon da suka ba shi be tasiri ba.
Cikakken bayanin jami'in da abun ya faru da shi, matashi mai matsakaicin shekaru, bai samu ba a halin yanzun da muke kawo muku rahoto.
Me ya yi sanadin mutuwarsa?
Hakanan har yanzun ba'a gano musabbabin abin da ya yi sanadin mutuwar jami'in nan take ba ko kuma wani sanadi da yake fama da shi tun baya.
Amma wani babban ma'aikaci a hukumar LASTMA ya tabbatar mana da faruwar lamarin bisa sharaɗin boye bayanansa.
Ya ce tuni aka kawar da gawarsa zuwa Asibitin koyarwa na jami'ar jihar Legas LASUTH da ke babban birnin jiha, Ikeja.
A wani labarin na daban kuma Muhimman abubuwan da ya kamata kowane ɗalibi ya sani game da JAMB da za'a fara Gobe Jumu'a
A gobe Jumu'a 6 ga watan Mayu ɗalibai zasu fara zama jarabawar JAMB 2022 kuma za'a kammala ranar Asabar 14 ga watan Mayu.
Akwai muhimman abubuwa da muka tattara muku wanda ya zama wajibi kowane mai niyyar zama jarabawar ya sani kafin lokacin.
Asali: Legit.ng