Bayan zukekiyar budurwa ta kama dakin otal da gungun samari, an tsinci gawarta

Bayan zukekiyar budurwa ta kama dakin otal da gungun samari, an tsinci gawarta

  • Wata budurwa mai shekaru dab da 30 ta sheka barzahu, an tsinci gawarta kwance a dakin wani Otel dake Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi
  • An gano yadda wacce lamarin ya auku da ita ta isa Otel din ita da wasu gungun maza masu karancin shekaru a cikin duhun dare
  • Daga bisani, an tsinci gawarta a dakin bayan an balle kofar a ranar inda aka tarar sun yi mata aika-aika ta hanyar amfani da kwararan robobi

Ebonyi - Wata budurwa mai shekaru kusan 30, mai suna Ugochi Nworie ta rasa rayuwarta sanadiyyar hadaka wurin yi ma ta fyade a wani Otel cikin Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi da wasu samari suka yi.

An gano yadda wacce lamarin ya auku da ita ta isa Otel din tare da wasu maza a duhun dare, jaridar The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

Bayan zukekiyar budurwa ta kama dakin otal da gungun matasa, an tsinci gawarta
Bayan zukekiyar budurwa ta kama dakin otal da gungun matasa, an tsinci gawarta. Hoto daga thenationonlineng.net
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daga bisani aka tsinci gawar budurwar a dakin Otel din, bayan an balle kofar a ranar. An tarar da an daure ma ta kafafu, hannaye da baki.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Loveth Odah, wacce ta tabbatar da aukuwar lamarin, ta ce ana kokarin ganin an zakulo wadanda suka tafka aika-aikar, sannan suka bar dakin Otel din ba tare da an gane ba.

An tsinci kwararon robobi da aka yi amfani dasu a dakin yayin bincikar shi da aka yi.

An tsinta gawar magidanci da budurwa a mota, sun mutu suna tsaka da 'kece-raini'

A wani labari na daban, an tsinta gawar wani mutum da wata mata wadanda aka gano sun mutu a cikin mota kirar SUV yayin da suke tsaka da jima'i.

The Nation ta ruwaito cewa, an tsinta gawarsu a daren Lahadi a rukunin gidaje na Jakande da ke Isolo a jihar Legas yayin da makwabta da suka balle motar bayan sun lura da injinta a kunne tun daga ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

Mutumin mai suna Koyejo ya dauka masoyiyarsa wacce ba a san sunanta ba yayin da yake hanyarsa ta zuwa gidan iyayensa da ke rukunin gidaje na Jakande a Isolo kamar yadda abokansa suka yi ikirari.

Vanguard ta ruwaito cewa, ya siya tsire kafin ya tsayar da motarsa daidai Double Star domin ya dan shakata a cikin motar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng