Ba gaskiya bane ace komai na tafiya dai-dai a Najeriya, inji Obasanjo
- Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya ce babu abin da ke tafiya dai-dai a Najeriya, amma wataran komai me wucewa ne
- Sai dai Obasanjo ya bukaci kowane ɗan Najeriya ya ƙara imani da Allah domin wataran zai duba kuma ya yi wa ƙasar nan rahama
- Tsohon shugaban ya ce ba Najeriya kaɗai bane ke fama da ƙalubale, lamarin ya shafi duniya ne baki ɗaya
Ogun - Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana yaƙininsa cewa ko wane irin muni halin Najeriya ya kai, komai zai zama tarihi watarana, kamar yadda Premium Times ta rahoto.
Obasanjo, wanda ya yi wannan furucin ne a wurin wani taro da Cocin Deeper Life ta shirya a Abeokuta kuma aka watsa shi kai tsaye ranar Talata, ya roki yan Najeriya su ƙara imani da Allah.
Tsohon shugaban ya ce duba da hali da yanayin da ake ciki, Najeriya da kuma duniya baki ɗaya na buƙatar Allah ya kawo ɗauki, bisa haka ya roƙi 'ya'yan Allah su kai masa kukan su.
Obasanjo ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Idan ka duba abubuwan dake faruwa birane, jihohin mu, ƙasar mu, nahiyar mu ta Afirka da sauran sassan duniya, baki ɗaya duniya tana bukatar jahadin yanayi."
"Wasu mutane sun zarge mu, Kiristoci da imanin su bai kai ko ina ba, haka duniyar take tun lokacin Annabi Isah, amma hakan na nufin mu cire tsammani? A'a."
"Babu wani lokaci ko wani zamani da aka yi a tarihin duniya wanda ba masu imani bane suka tsaya kai da fata har komai ya wuce."
Ta ya Najeriya zata tsallake wannan yanayin?
Obasanjo ya ƙara da cewa Annabi Nuhu ya tsaya tsayin daka kan aikinsa da imaninsa a lokacinsa, Allah ya kira shi da mutum mai tsoron Allah kuma mai kauce wa saɓo, mutum mai gaskiya.
"Ina da yaƙinin cewa saboda irin waɗan nan mutanen kirkin maza da mata Allah zai kalli halin da muke ciki a Najeriya, ya mana rahama."
"Mutane marasa son gaskiya ne kaɗai zasu ce komai na tafiya dai-dai, amma waɗan da suka gaskata Allah suka yi Imani da Annabi Isa, komai zai wuce."
"Mu masu imani duk halin da muka tsinci kan mu duk muninsa kada mu zubar da imanin mu, kuma komai me wucewa ne."
A wani labarin kuma Ana shirin tunkarar 2023 jam'iyyar PDP ta gamu da cikas, Wani Sanata mai ci ya fice daga jam'iyyar
Yayin da kowace jam'iyyar siyasa ke ƙoƙarin dinke ɓarakarta domin tunkarar 2023, PDP ta yi sake Sanata ɗaya tilo daga Oyo ya yi murabus.
Sanata Kola Balogun, mai wakiltar Oyo ta Kudu ya aike wa PDP wasikar murabus daga kasancewarsa ɗan jam'iyya.
Asali: Legit.ng