Bikin karamar sallah: Osinbajo ya ziyarci Kano don yin Hawan Daba

Bikin karamar sallah: Osinbajo ya ziyarci Kano don yin Hawan Daba

  • A yau Talata, 3 ga watan Mayu, ne masarautar Kano ta yi hawan daba daga cikin bukukuwan karamar sallah
  • Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinabjo ma ya halarci bikin tare da gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje
  • A kan yi bikin Hawan Daba ne a kasar Hausa don sada muzunci tsakanin sarakuna a lokacin bikin sallah ko kuma yayin tarbar wani babban bako

Kano - Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ziyarci jihar Kano domin yin Hawan Daba na karamar sallah.

An yi hawan ne a fadar mai martaba sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, a yau Talata, 3 ga watan Mayu.

Bikin ya samu halartan manyan mutane kamar su gwamnan jihar, Dr Abdullahi Umar Ganduje tare da sauran masu fada aji a gwamnati.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Hadimin Buhari, Bashir Ahmad ya yi murabus daga kujerarsa

Hotunan Osinbajo yayin da ya halarci Hawan Daba na masarautar Kano
Hotunan Osinbajo yayin da ya halarci Hawan Daba na masarautar Kano Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

A kan yi bikin Hawan Daba ne a kasar Hausa don sada muzunci tsakanin sarakuna a lokacin bikin sallah ko kuma yayin tarbar wani babban bako.

A wannan biki na Daba sarakuna kan hadu da su da hakimansu kowane da tawagarsa su hau dawakai cikin ado na kece raina, haka nan ma dawakan nasu za a caba musu ado.

Wannan biki na Hawan Daba wata hanya ce ta kulla zumunci tsakanin sarakuna da kuma nuna wa bakon da ake karramawa dadaddiyar al’adar ta mallam Bahaushe.

Ga karin hotuna na hawan a kasa:

Hotunan Osinbajo yayin da ya halarci Hawan Daba na masarautar Kano
Hotunan Osinbajo yayin da ya halarci Hawan Daba na masarautar Kano Hoo: @MobilePunch
Asali: Twitter

Hotunan Osinbajo yayin da ya halarci Hawan Daba na masarautar Kano
Hotunan Osinbajo yayin da ya halarci Hawan Daba na masarautar Kano Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Hotunan Osinbajo yayin da ya halarci Hawan Daba na masarautar Kano
Hotunan Osinbajo yayin da ya halarci Hawan Daba na masarautar Kano Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

Bikin Sallah: Hotunan Gwamna El-Rufai yayin da ya halarci Hawan Bariki

A wani labarai makamancin wannan, mun kawo cewa a yau Talata, 3 ga watan Mayu ne masarautar Zazzau ta gudanar da bikin hawa na karamar sallah a garin Zaria da ke jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Billahil lazi la ilaha illahuwa za mu rike maka amanarka – Gawuna ga Ganduje

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru Ahmad El-rufai, yana daga cikin manyan mutanen da suka halarci Hawan Barikin karkashin jagorancin Mai martaba sarkin Zazzau, Malam Ahmad Nuhu Bamalli.

El-rufai ya kuma lura da soyayya na musamman da mutanen yankin da dama ke yiwa masarautar ta zazzau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel