Bikin Sallah: Hotunan Gwamna El-Rufai yayin da ya halarci Hawan Bariki
- Masarautar Zazzau ta gudanar da Hawan Bariki daga cikin bukukuwan karamar sallah
- Hawan sallan wanda aka yi a garin Zaria a yau Talata, 3 ga watan Mayu, ya samu halartan gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai
- El-Rufai ya mika godiya ga sarkin Zazzau, Malam Ahmad Nuhu Bamalli da majalisar masarautar kan shirya wannan taro da suka yi
Kaduna - A yau Talata, 3 ga watan Mayu ne masarautar Zazzau ta gudanar da bikin hawa na karamar sallah a garin Zaria da ke jihar Kaduna.
Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru Ahmad El-rufai, yana daga cikin manyan mutanen da suka halarci Hawan Barikin karkashin jagorancin Mai martaba sarkin Zazzau, Malam Ahmad Nuhu Bamalli.
El-rufai ya kuma lura da soyayya na musamman da mutanen yankin da dama ke yiwa masarautar ta zazzau
A wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter, gwamnan ya mika godiya ga sarki da masarautar ta zazzau a kan shirya wannan kayataccen biki.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ga karin hotuna daga bikin a kasa:
Shafin gwamnan ya rubuta:
"A yau ne Malam Nasir @elrufai ya kai ziyara Zariya domin Hawan Bariki. Ya lura da soyayya na musamman da al’umma da dama ke yiwa wannan masarauta, ya kuma gode wa Mai Martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmad Nuhu Bamalli da Majalisar Masarautar Zazzau kan wannan gagarumin taron."
Sallah: Masarauta ta dakatar Hakimai, ‘Dan Majalisa bayan hawan idi saboda saba doka
A gefe guda, mun ji cewa mai martaba Sarkin Zazzau, Amb. Ahmed Nuhu Bamalli ya dakatar da wasu Hadimai hudu jim kadan bayan an sauko daga karamar sallah.
Daily Trust ta ce wannan sanarwa ta fito ne daga bakin mai magana da yawun masarautar Zazzau da ke jihar Kaduna, Abdullahi Aliyu Kwarbai.
A ranar Litinin, 2 ga watan Mayu 2022, Alhaji Kwarbai ya ce dakatarwar da aka yi wa wadannan sarakai za ta fara aiki ba tare da wani bata lokaci ba.
Asali: Legit.ng