Zamfara: Mummunar gobara ta lamushe ofishin hukumar INEC

Zamfara: Mummunar gobara ta lamushe ofishin hukumar INEC

  • Gagarumar gobara ta kama a ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC a daren Litinin, ranar sallah
  • Ganau sun tabbatar da cewa ko tsinke ba a cire a ofishin ba saboda jami'an kashe gobara sun bayyana amma babu ruwa a tankinsu
  • Jama'a sun tabbatar da cewa gobabar ta fara wurin karfe 9 na dare a ofishin INEC da ke karamar hukumar Kauran Namoda

Zamfara - Mummunar gobara ta lamushe daya daga cikin ofisoshin hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC da ke jihar Zamfara.

Ofishin da lamarin ya shafa ya na nan a karamar hukumar Kauran Namoda da ke jihar Zamfara kamar yadda mazauna yankin suka sanar, Channels TV ta ruwaito.

Daga hukumar 'yan sanda har hukumar zabe mai zaman kanta ba su tabbatar da aukuwar lamarin a jihar ba kuma ba su tabbatar da cewa ko an samu wanda ya rasa ransa a yayin rubuta wannan rahoton.

Kara karanta wannan

An kuma, Bam ya tashi a kusa da sansanin Sojojin Najeriya a babban birnin jihar Arewa

Zamfara: Mummunar gobara ta lamushe ofishin hukumar INEC
Zamfara: Mummunar gobara ta lamushe ofishin hukumar INEC. Hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC

Ofishin shugaban fannin yada labarai na hukumar INEC na jihar Zamfaran an kasa samunsu a waya duk da kokarin da aka dinga yi na jin bakinsu.

A yayin bayyana yadda lamarin ya faru, mazauna yankin sun sanar da Channels TV cewa gobarar ta fara ne wurin karfe 9 na daren Litinin inda ta kurmushe kusan dukkan ginin.

Sun bayyana cewa duk da jami'an hukumar kashe gobara sun bayyana a wurin da wuri domin kashe wutar, ba a samu nasarar yin hakan ba saboda rashin isasshen ruwa a tankinsu.

Yayin da aka kasa gane musababbabin gobarar a take, wani ganau ya sanar da Channels TV ta wayar tarho cewa a ranar Talata sun gane cewa babu abinda aka cire daga ofishin hukumar zaben.

Kara karanta wannan

Rahoton gwamnati: Mutanen Legas kadai na cin naman shanu na N328bn a duk shekara

Gobara ta kama ofishin hukumar INEC a jihar Enugu

A wani labari na daban, gobara ta kama ofishin hukumar shirya zabe ta kasa watau INEC dake Obollo-Afor, karamar hukumar Udenu a jihar Enugu.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Daniel Ndukwe, ya tabbatar da hakan ga NAN ranar Juma'a. Ndukwe ya ce wannan gobarar ta faru ne misalin karfe 9:40 na dare Alhamis.

Yace: "Hukumar ta samu kira a ofishinta dake Udenu inda aka ce wuta ya tashi a ofishin INEC dake Obollo-Afor."
"Jami'an yan sandan dake wajen suka garzaya wajen da wuri, yayinda aka tuntubi hukumar kwana-kwanan yankin don kashe wutan."

Asali: Legit.ng

Online view pixel