Da duminsa: Gobara ta kama ofishin hukumar INEC a jihar Enugu

Da duminsa: Gobara ta kama ofishin hukumar INEC a jihar Enugu

- Ofishoshin INEC akalla 12 sun kone yanzu tsakanin 2019 da 2021

- Yan ta'addan IPOB/ESN na kai hare-hare ofishohin a yankin kudu maso gabas

- Ana tsoron da kamar wuya a iya gudanar da zaben 2023 a yankin idan haka ya cigaba

Gobara ta kama ofishin hukumar shirya zabe ta kasa watau INEC dake Obollo-Afor, karamar hukumar Udenu a jihar Enugu.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Daniel Ndukwe, ya tabbatar da hakan ga NAN ranar Juma'a.

Ndukwe ya ce wannan gobarar ta faru ne misalin karfe 9:40 na dare Alhamis.

Yace: "Hukumar ta samu kira a ofishinta dake Udenu inda aka ce wuta ya tashi a ofishin INEC dake Obollo-Afor."

"Jami'an yan sandan dake wajen suka garzaya wajen da wuri, yayinda aka tuntubi hukumar kwana-kwanan yankin don kashe wutan."

Da duminsa: Gobara ta kama ofishin hukumar INEC a jihar Enugu
Da duminsa: Gobara ta kama ofishin hukumar INEC a jihar Enugu Hoto: Leadership Newspaper
Asali: Facebook

DUBA NAN: Wajibi ne Buhari ya saurari abinda muke fada masa, Gwamnonin Kudu 17

Ya ce sakamakon kokarin jami'an yan sanda, na kwana-kwana da jama'an dake wajen, an samu nasarar kashe wutan kafin ya kama sauran ofishohin dake wajen.

"Binciken da aka fara kaddamarwa ya nuna cewa wutan lantarki ya haddasa gobaran saboda kawo wutan da akayi," kakakin ya kara.

Ya ce kwamishanan yan sandan jihar, Mohammed Aliyu, ya bada umurnin kaddamar da bincike.

Wannan gobara ya biyo bayan banka wutan da akayia ofishohin INEC dake Akwa Ibom da Abia.

Da duminsa: Gobara ta kama ofishin hukumar INEC a jihar Enugu
Da duminsa: Gobara ta kama ofishin hukumar INEC a jihar Enugu Hoto: Leadership Newspaper
Asali: Facebook

KU KARANTA: Muna namijin kokarin wajen magance matsalar tsaro, ina fatan yan Najeriya zasu gane, Buhari

Da duminsa: Gobara ta kama ofishin hukumar INEC a jihar Enugu
Da duminsa: Gobara ta kama ofishin hukumar INEC a jihar Enugu Hoto: Leadership Newspaper
Asali: Facebook

A bangare guda, Sarkin Musulmi, Sultan Alhaji Sa'ad Abubakar III ya kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnoni da su kawo karshen rashin tsaro a kasar nan, Jaridar The Nation ta wallafa.

Sarkin Musulmin wanda shine shugaban majalisar koli ta al'amuran addinin Musulunci a Najeriya, yayi wannan jawabin ne a Sokoto bayan sallar idin karamar sallah da aka yi a ranar Alhamis da ta gabata.

Ya ce: "Muna kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da dukkan gwamnonin jihohi da su gaggauta kawo karshen rashin tsaro da ya addabi kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng