Dakarun NAF da AIB sun mamaye wurin da jirgin sama yayi hatsari a Kaduna

Dakarun NAF da AIB sun mamaye wurin da jirgin sama yayi hatsari a Kaduna

- Dakarun sojin saman Najeriya tare da jami'an AIB sun mamaye inda jirgin sama yayi hatsari

- Kamar yadda hukumar filin sauka da tashin jiragen saman Najeriya ta sanar, sojin sun rufe yankin domin bincike

- An gano cewa da farko jirgin zai sauka sansanin sojin sama dake Mando amma sai ya waske zuwa na Kaduna saboda yanayin gari

Sojoji sun rufe yankin da jirgin dakarun sojin saman Najeriya yayi hatsari a ranar Juma'a a filin suaka da tashin jiragen sama na Kaduna.

Jirgin saman wanda ke dauke da shugaban sojin kasa na Najeriya, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru da wasu manyan sojoji ya fadi a filin jirgin inda ya kashe dukkan mutum 11 da ke ciki har da matukan jirgin.

A yayin jawabi kan lamarin, manajan filin jirgin sama na Kaduna, Amina Salami ta sanar da Channels TV cewa hukumar sojin Najeriya sun mamaye yankin da lamarin ya auku.

KU KARANTA: Yadda Labarin mutuwar Shekau ya jefa mazauna Maiduguri nishadi da hamdala

Dakarun NAF da AIB sun mamaye wurin da jirgin sama yayi hatsari a Kaduna
Dakarun NAF da AIB sun mamaye wurin da jirgin sama yayi hatsari a Kaduna. Hoto daga @ChannelsTV
Asali: Twitter

KU KARANTA: Jawabin karshe da Laftanal Janar Attahiru yayi wa dakarun sojin Najeriya

Ta kara da cewa jirgin sojin da farko an yi zai sauka ne sansanin sojin saman Najeriya dake yankin Mando amma daga baya ya waske inda ya sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na Kaduna saboda yanayin gari mara kyau.

Kamar yadda tace, hukumar binciken hadurra ce zata gano musabbabin faduwar jirgin saman.

Legit.ng ta ruwaito, hedkwatar tsaro ta kasa ta bayyana dalilin da ya kawo tarwatsewar jirgin sama wanda yayi sanadiyyar mutuwar shugaban sojojin kasa na Najeriya, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru da wasu sojoji 10 a ranar Juma'a, 21 ga watan Mayun 2021.

Kamar yadda Onyema Nwachukwu, mai magana da yawun hedkwatar tsaro ya sanar, duk da ana cigaba da binciken sanadin lamarin, hatsarin ya auku ne bayan jirgin ya sauka a filin sauka da tashin jiragen saman na Kaduna.

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga matukar damuwa a kan hatsarin jirgin sama da yayi ajalin shugaban dakarun sojin kasa, Laftanal Janar Ibrahim Attahiru da wasu manyan sojoji.

Kamar yadda mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya bayyana alhinin da shugaban kasan ya shiga.

"A yayin addu'a ga Ubangiji da ya gafartawa rayukan masu kishin kasan, shugaban kasan yace wannan babban rashi ne yayin da dakarun sojin kasar nan suka zage wurin ganin karshen kalubalen tsaron da kasar nan ke fuskanta," Shehu ya wallafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel