Ranar Ma'aikata: Gwamna a Najeriya ya ƙara mafi karancin Albashi zuwa N40,000

Ranar Ma'aikata: Gwamna a Najeriya ya ƙara mafi karancin Albashi zuwa N40,000

  • Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya kara wa ma'aikatan jiharsa mafi karancin Albashi daga N30,000, zuwa N40,000
  • Gwamnan ya ce sanin kowa matsin tantalin arziƙi ya sa Albashin ba iya isar ma'aikaci da iyalansa
  • Ya kuma sanar da tsofaffin ma'aikata cewa gwamnatinsa ta fara shirin yadda za'a biya su basukan da suke bi

Edo- Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya ƙara mafi karancin albashi ga ma'aikatan jiharsa daga N30,000 da gwamnatin tarayya ta ƙayyade zuwa N40,000.

Daily Trust ta rahoto cewa gwamnan ya bayyana wannan ƙarin ne yayin taya ma'aikata murnar 'Ranar ma'aikata ta duniya' ranar Lahadi 1 ga watan Mayu, 2022.

Gwamnan Edo, Godwin Obaseki.
Ranar Ma'aikata: Gwamna a Najeriya ya ƙara mafi karancin Albashi zuwa N40,000 Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Gwamna Obaseki ya ce:

"Kamar yadda kowannen mu ya sani, Naira N30,000 kawai ba zai ɗauki ma'aikaci da iyalansa ba, ba dai-dai bane mu cigaba da nuna halin ko in kula, mu yi kamar ba mu san ma'aikatan mu na shan wahala ba."

Kara karanta wannan

Dalibai mata na jami'o'i biyu a Arewa zasu fito tituna zanga-zanga tsirara kan yajin aikin ASUU

"Gwamnatin jihar Edo ta yanke sake duba mafi ƙarancin Albashi kuma ta ƙara shi daga N30,000 zuwa N40,000 a kowane wata. Babu kokwanto Edo ce jiha ta farko da ta bullo da wannan tun bayan ɓarkewa cutar COVID19."

Gwamna Obaseki ya kuma ƙara da cewa gwamnatinsa ta shirya yin duk abinda ya dace domin ganin ta inganta rayuwar ma'aikatanta.

Zamu biya ƴan Fansho haƙƙoƙin su - Obaseki

Dadin daɗawa, gwamnan ya ce gwamnatinsa ta nuna sha'awar biyan tsofaffin ma'aikata baki ɗaya kuɗaɗen da suke bi duk da gwamnatin baya ta rike musu hakokin su.

"Duba da yanayin faɗi tashin tattalin arziki, Na amimce daga wannan watan na Mayu, za'a fara biyan yan Fasho hakkokin su ta yadda muka yi yarjejeniya da kungiyar yan Fansho ta ƙasa, wanda zai fara aiki daga Mayu, 2022."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Bayan gana wa da Buhari, Wani Minista ya janye kudirinsa na takarar shugaban ƙasa

A wani labarin kuma Jam'iyyar PDP ta lashe kujerun Ciyaman 23 da Kansiloli 276 a jihar Benuwai

Jam'iyyar PDP ta yi nasarar lashe dukkan kujeru a zaɓen kananan hukumomin jihar Benuwai da aka gudanar ranar Asabar.

Shugaban hukumar zaɓe ta jihar, Tersoo Loko, yayin sanar da sakamakon ranar Lahadi, ya ce PDP ta lashe ciyaman 23 da Kansiloli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262