Sabon Sarkin Oyo zai gaje matan Oba Lamidi 11, Yarima mai jiran gado Ladigbolu

Sabon Sarkin Oyo zai gaje matan Oba Lamidi 11, Yarima mai jiran gado Ladigbolu

  • Daya daga cikin Yarimomin da ka ya zama sabon Alaafin of Oyo ya yi bayani game da mata sama da 11 da tsohon Sarki Lamidi ya bari
  • A cewarsa, bisa al'ada, sabon sarkin ne zai debi ganimar matan amma tun da zamani yazo, zasu iya gyara
  • Gidan Ladigbolu na cikin jerin gidajen da zasu gabatar da masu takara neman kujerar sabon sarkin

Oyo - Archbishop Emeritus na Cocin Methodist, Rabaran Ayo Ladigbolu, ya yi bayani game da al'adar fadar Oba na Oyo na kuma abinda zai faru da matan da marigayi Oba Lamidi ya bari.

Ayo Ladigbolu wanda yake daya daga cikin wadanda ka iya zama sabon Sarkin, a hirarsa da jaridar Punch yace amma duk da wannan al'ada za'a iya barinsu su tafi.

A cewarsa:

"Sabon Sarkin ne zai gajesu kuma wannan shine al'ada, amma ka san abubuwa na canzawa yanzu. "

Kara karanta wannan

Abin Da Yasa Ƴan Siyasa Ke Ɗaukan Alkawurran Da Ba Za Su Iya Cika Wa Ba, Ɗan Majalisar Najeriya

"Idan mace ta auri Alaafin, toh auren har abada ne. Amma tun da rayuwa na canzawa yanzu, zamu iya wani gyara."

Ayo Ladigbolu ya kara da cewa kujerar Sarki suka aura ba mutum ba saboda haka duk wanda ya zama sarki ne zai rika kula da su.

Yayinda aka tambayesa shin idan wata cikinsu tace ba ta son sabon sarkin ma zai faru? yace:

"Ba sai na yi dogon bayani ba; matan kujerar sarauta ne. Amma dai zamu iya wasu sauye-sauye."

Ladigbolu
Sabon Sarkin Oyo zai gaje matan Oba Lamidi 11, Yarima mai jiran gado Ladigbolu Hoto: Punch
Asali: Facebook

Jerin sunaye da hotunan mata 11 da marigayi Sarkin Oyo, Oba Lamidi, ya bari

Sarkin, lokacin rayuwarsa ya shahara da auren mata da yawa kuma dukka farare.

Oba Lamidi lokuta da dama ya kan fito da matansa sanye cikin kayan anko kuma yana alfahari da su.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan Shi'a da jamian tsaro sun yi arangama, soji sun harbi mutum 8 a Zaria

Ya mutu ya bar mata 11 da ya aura, kuma babbar uwargidarsa ita ce Ayaba Abibat Adeyemi.

Legit ta tattaro muku sunaye da hotunan matan Oba Lamidi.

Kallesu nan

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel