Kotu ta tasa keyar Muhyi RiminGado gidan yari, ta bada sharrudan beli
- Gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da Muhyi Magaji Rimin Gado gaban kotun majistare yau Juma'a, Alkali ya ce a jefashi gidan yari
- Wannan ya biyo bayan damkeshi da Yan sanda suka yi a Abuja ranar Alhamis kuma suka tafi da shi Kano
- Ana zargin Rimin Gado ya aikata wasu laifuka amma ya ki gurfana gaban majalisar dokokin Kano
Kano - Kotu ta bada umurnin tasa keyar tsohon shugaban hukumar korafe-korafe da yaki da rashawa jihar Kano, Muhyi Magaji Rimin Gado, kurkuku ranar Juma'a, 29 ga Afrilu, 2022.
Wannan ya biyo bayan gurfanar da shi da gwamnatin jihar tayi a kotun majistare.
A cewar Daily Nigerian, Muhyi ya bayyanawa kotu cewa bai da laifin zargin da ake masa na bada bayanin karya.
A karshe, Alkalin kotun, Aminu Gabari, ya bada belin Rimingado kan N500,000 da masu tsaya masa biyu.
Alkalin yace wajibi ne mutane biyun da zasu tsaya masa su kasance mahaifinsa da kawunsa kuma su gabatar da hujjar cewa sun biya haraji shekaru uku da suka gabata.
Kotu tace ya sha zaman gidan yari har sai an cika sharrudan belin.
Kalli bidiyon lokacin da ake kaishi kurkuku:
An damke tsohon shugaban hukumar rashawa a Kano, Muhyi Rimin Gado
Jami'an hukumar yan sanda sun damke tsohon shugaban hukumar korafe-korafe da yaki da rashawa a jihar Kano PCACC, Muhuyi Magaji Rimin Gado.
Daily Nigerian ta ruwaito cewa an damke Rimin Gado ne a masaukin gwamnan jihar Sokoto dake birnin tarayya Abuja.
An tattaro cewa ya je gidan masaukin ne halartan zaman tantance yan takaran gwamnan jihar Kano karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP.
Daga nan aka garzaya da shi Kano don gurfana gaban hukuma.
Laifin me Rimin Gado yayi
A watan Yulin 2021 aka dakatad da Muhyi Magaji daga kujerarsa ta shugaban hukumar yaki da rashawa bayan ya kaddamar da binciken wasu badakalan kwangila da aka baiwa wasu kamfanoni masu alaka da iyalan gwamnan jihar Kano.
Daga baya majalisar dokokin jihar ta bukaci Rimin Gado ya gurfana gabanta don gudanar da bincike kansa amma yaki halarta saboda rashin lafiyar da yake fama da ita.
A sakon da ya aikewa majalisar ya hada da takardar shaidar asibiti na nuna cewa ba shi da lafiya.
Amma ranar 19 ga Yuli, 2021, bisa bukatar majalisar, Asibitin tarayya dake Abuja ya aike wasika majalisar dokokin Kano cewa takardun rashin lafiyar da Rimin Gado ya gabatar na bogi ne.
A takarda mai lamba NHA/CMAC/GC/0117/2021/V.I/01, diraktan harkokin jinya a asibitin tarayya, Dr. A.A. Umar, yace sun yi bincike kuma sun gano takardun bogi ne.
Asali: Legit.ng