Gwamnati Zamfara Ta Gurfanar Da Sarakunan Da Ta Tube Wa Rawani Kan Taimakon 'Yan Ta'adda

Gwamnati Zamfara Ta Gurfanar Da Sarakunan Da Ta Tube Wa Rawani Kan Taimakon 'Yan Ta'adda

  • An gurfanar da sarakuna biyu na jihar Zamfara da aka tsige su daga mukamansu kan zargin hada kai da yan bindiga
  • Bayan gurfanar da su a kotun, lauya mai kare su ya nemi a bada su beli domin yawan shekarunsu da kuma rashin lafiya
  • Alkalin kotun shari'ar da aka gurfanar da su ya amince da bada belin amma ya gindaya sharruda kafin belin da za su cika

Zamfara - Gwamnatin Jihar Zamfara ta gurfanar da sarakuna biyu da aka tsige saboda zargin taimakawa yan bindiga a kotun majistare ta jihar, Channels TV ta rahoto.

An gurfanar da su ne kan tuhumar aikata laifuka biyar da suka shafi hadin baki don aikata laifi, dakile hujoji, mallakar kadarori ba bisa ka'ida ba, da hada kai da yan bindiga.

Kara karanta wannan

Eid-el-Fitr: Gwamnatin tarayya ta bayyana ranaku 2 na hutun Sallah

Gwamnati Zamfara Ta Gurfanar Da Sarakunan Da Ta Tube Wa Rawani Kan Taimakon 'Yan Ta'adda
Gwamnati Zamfara Ta Gurfanar Da Sarakunan Da Ta Tube Wa Rawani. Hoto: The Punch.
Asali: UGC

An gurfanar da su ne a gaban babban majistare ne kotu ta 1 na jihar Zamfara inda Mai shari'a Saadu Garba ya saurari tuhume-tuhumen kamar yadda News Express ta rahoto.

Lauyoyi masu kare sarakunan biyu sun ki amincewa a kotun ta saurari karar inda suka kafa hujja da doka ta 7 na Jihar Zamfara, 1019 wacce ta ce ba za a iya yi wa musulmi shari'a a kotun majistare ba, hakan yasa aka mika shari'ar zuwa babban kotun shari'a.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Alkalin kotun shari'a ta 1, Samaru, Gusau, Mai shari'a Hadi Sani, ya bada belin sarakunan biyu bayan lauyoyinsu sun mika bukatan bada belin kan dalilin tsufa da rashin lafiya duba da cewa an tsare su tsawon wata 10 zuwa 11.

Kotu ta bada belinsu saboda rashin lafiya

Kotun ta umurci sarakunan gabatar da mutum 3 da za su karbi belinsu, su kasance fitattun yan kasuwa, fitattun malaman addini, ko babban ma'aikacin gwamnati wanda ke da N100m.

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan sanda sun yi ram da 'yan ta'adda 2 dauke da miyagun makamai

Za su cigaba da zama a jihar kuma sai sun nemi izinin kotu duk lokacin da suke bukatar zuwa asibiti.

Lauya mai gabatar da kara, Aliyu Alkali ya nuna kin amincewa da bada belin sarakunan biyu yana mai cewa an gurfanar da su ne saboda hannu kan harin yan bindiga.

Ya ce doka ta bawa kotun ikon bada belin ko hana wa don haka ba su da matsala idan an bada belin sarakunan na Zamfara.

Jagoran lauyoyin sarakunan, Bello Usman, ya nuna gamsuwa da belin da aka bawa sarakunan da aka tsige duba da cewe sun kasance tsare tsawon watanni.

'Yan Ta'addan Da Suka Kai Hari Sansanin Sojoji Na Kaduna Sun Ɗanɗana Kuɗarsu, Lai Mohammed

A bangare gudan, Gwamnatin Tarayya, a ranar Laraba ta ce yan ta'addan da suka kai hari sansanin sojoji da ke Birnin Gwari a Kaduna sun sha azaba a hannun sojoji a yayin da suka fatattake su, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Majalisar dattawa ta haramta biyan masu garkuwa da mutane kudin fansa

Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke amsa tambayoyi kan tsaro bayan taron FEC da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a Aso Villa a Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa sojoji 11 ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da wasu da dama suka jikkata yayin harin na ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164