Yaƙin Rasha da Ukraine yana cutar da mutane da yawa, muna bukatar a samu maslaha, Buhari

Yaƙin Rasha da Ukraine yana cutar da mutane da yawa, muna bukatar a samu maslaha, Buhari

  • Shugaba Buhari ya bukaci a gaggauta nemo hanyar warware rikicin Rasha da Ukraine don gudun illar lamarin ga sauran al'umma
  • Shugaban ƙasan ya ce yaƙin ya ɗauki dogon lokaci fiye da tsammani kuma ya shafi mutane, ya cutar da su
  • Buhari ya yaba da jajircewar Sakataren majalisar ɗinkin duniya a yunkurinsa na ganin an tsagaita wuta

Abuja - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ce akwai bukatar samar da maslaha cikin gaggawa da zata kawo karshen yaƙin Rasha-Ukraine domin shawo kan illar da yake wa al'umma.

Yaƙin Rasha-Ukarine, wanda aka fara ranar 24 ga watan Favrairu, ya lakume rayukan ɗaruruwan mutane, yayin da wasu miliyoyi suka rasa mahallansu.

Da yake jawabi ranar Alhamis a wurin buɗe bakin da aka shiryawa wakilan diplomasiyya a Najeriya, Buhari, ya ce yaƙin ya ɗauki dogon lokaci, kamar yadda The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Bayan Yahaya Bello, wani gwamnan APC ya lale Miliyan N100m ya sayi Fom ɗin takarar shugaban kasa na APC

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Yaƙin Rasha da Ukraine yana cutar da mutane da yawa, muna bukatar a samu maslaha, Buhari Hoto: Buhari Sallau/facebook
Asali: Facebook

Buhari ya kara da cewa ya kamata ƙasashen duniya su yi karatun ta natsu kuma su shiga lamarin domin tasirin da ya yi wa walwalar mutane.

Shugaban ƙasa ya ce:

"Yaƙin ya ɗauki dogon lokaci, ya lakume abubuwa da yawa, ya cutar da mutane fiye da yadda aka yi tsammani. A hankali duniya na ƙara fuskantar illar rikicin kuma zai cigaba da ƙara muni ne idan ba'a ɗauki mataki ba."

Buhari ya yaba wa UN

Shugaba Buhari ya yaba wa Sakatare Janar na majalisar ɗinkin duniya (UN), Antonio Gutteres, bisa jajircewarsa har ya kai ziyara biranen Moscow da Kyiv a yunkurin ganin an tsagaita wuta.

"Wajibi majalisar dinkin duniya ta cigaba da jan ragamar tattaunawa wacce muke fatan zata iya dawo da zaman lafiya ta hanyar diplomasiyya."

Kara karanta wannan

Abubuwan da shugaba Buhari ya faɗa mun har na ayyana shiga takarar shugaban ƙasa, Gwamnan APC

Ya kuma roƙi mutanen duniya musamman Musulmai su yi amfani da watan Ramadana wajen yin addu'ar kawo ƙarshen yakin da kuma dawowar zaman lafiya a sassan duniya.

A wani labarin na daban kuma Ana Shirin Sallah, Yan bindiga sun kashe Kwamandan jami'an tsaro, sun tarwatsa mutanen gari a Zamfara

Miyagun yan bindiga sun yi awon gaba da Magajin Garin Rijana tare da wasu manoma a jihar Kaduna.

Mazauna ƙauyen sun bayyana cewa maharan sun tuntuɓi shuwagabannin al'umma, sun lissafo abubunwan da suke so a matsayin fansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262