Tallafin abinci: Gwamnatin Borno ta damke mutum 26 da ke karbar cin hanci daga IDPs mata
- Kwamitin raba kayan tallafi ga 'yan gudun hijira tayi ram da wasu 26 da suka nemi cin hanci daga mata marasa karfin da suka yi rigista karkashin shirin
- Shugaban kwamitin ya sanar da hakan ne yayin tunatarwa a kan cigaba da raba kayan abinci da kayayyakin amfani ga iyalai 100,000 a Maiduguri da kananan hukumomin Jere
- Ya bayyana yadda wasu mata suka kai kokensu ga kwamitin, tare da bayyana yadda wadanda ake zargin suka so amsar tsakanin kashi 50 zuwa 60 ba abun da gwamnati ta raba musu
Borno - A ranar Alhamis shugaban kwamitin raba kayan tallafi ga 'yan gudun hijira a jihar Borno, Saina Buba, ya tabbatar da yadda aka yi ram da wasu 26 da ake zarginsu da neman cin hanci daga mata marasa karfi da suka yi rijista karkashin shirin raba kayan tallafin.
Buba ya sanar da hakan ne yayin tunatarwa a kan cigaba da raba kayan abinci da kayayyakin amfani ga iyalai 100,000 a Maiduguri da kananan hukumomin Jere, Daily Nigerian ta ruwaito.
Ya labarta yadda mata suka shigar da korafi ga kwamitin, wanda hakan ne yasa kwamitin ta shaidawa 'yan sanda.
Shugaban kwamitin ya ce, 'yan sanda sun yi ram da wadanda ake zargin, yayin da ake cigaba da bincikar lamarin, rahoton Within Nigeria ya bayyana.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya jinjina wa matan da suka shigar da korafin, gami da shawartar saura da su cigaba da fallasa masu irin wannan dabi'ar ga hukumomin da suka dace.
Wasu daga cikin matan da hakan ya shafa, wadanda suka bukaci a sakaya sunayensu, sun bayyana yadda wadanda ake zargin suka nemi su basu kashi 50 da kashi 60 cikin dari na kayayyakin abincin da gwamanatin jihar ta raba musu.
"Daya daga cikin wadanda ake zargin ya bukaci N8,000 daga cikin N10,000, tirmin zani, sukari da sauran abubuwan da gwamnati ta bani.
"Ya bukaci in bashi wani kaso daga cikin abubuwan da aka bani, sannan in rike sauran," a cewarta.
Karfe 2 na dare, Zulum ya dira asibitin gwamnati na Monguno, zai kara 30% na albashi ga likitoci a LGs 7
A wani labari na daban, Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, yayin da ya kai ziyara babban asibitin a Konguno, ranar Asabar, ya sanar da amincewa da karin kashi 30 cikin dari na albashin likitoci a kananan hukumomi bakwai ba tare da tsammani ba.
Baya ga likitoci, ma'aikatan lafiya, anguwan zoma, masu gwaje-gwaje a dakin bincike, masu hada magunguna da sauran ma'aikatan lafiya na kananan hukumomi bakwai suma za su amfana da karin kashi 30 bisa dari na albashinsu, don karfafasu wajen gudanar da aiki mai nagarta da kula da fannin lafiya yadda ya dace.
Asali: Legit.ng