Hotunan matar basaraken Yarabawa da ta karba Musulunci, ta koma Khadija daga Joyce

Hotunan matar basaraken Yarabawa da ta karba Musulunci, ta koma Khadija daga Joyce

  • Matar babban basarake na kasar Ibadan, Joyce Anene Balogun, ta karba kalmar shahada inda ta koma Khadija Balogun
  • Lamarin ya faru ne a ranar Litinin, 25 ga watan Afirilu, a filin sallar Idin Ibadan yayin wata lakca ta watan Ramadan
  • Babban limamin Oyo, Sheikh Abdul Ganiyy Abubakary ne ya nakalta mata kalmar shahada sannan ya sanar a shafinsa na Facebook

Ibadan - Sarauniya Joyce Anene Balogun, matar basarake Olubadan na kasar Ibadan, Oba Lekan Moshood Balogun, ta karba kalmar shahada.

Sarauniyar ta karba kalmar shahada ne inda ta koma addinin Musulunci a wani wa'azin watan Ramadan da aka yi a ranar Litinin, 25 ga watan Afirilu a babban filin sallah na Ibadan karkashin shugabancin Honarabul Ibraheem Akintayo.

Hotunan matar basaraken Yarabawa da ta karba Musulunci, ta koma Khadija daga Joyce
Hotunan matar basaraken Yarabawa da ta karba Musulunci, ta koma Khadija daga Joyce. Hoto daga lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Babban limamin jihar Oyo, Sheikh Abdul Ganiyy Abubakary Agbotomokekere I, ya tabbatar da hakan a wallafar da yayi a shafinsa na Facebook inda ya kara da cewa sabon sunan sarauniyar shi ne Khadijah Mashood Lekan.

Kara karanta wannan

‘Dan Jam’iyya ya rubutawa Shugabannin APC takarda, yana so a hana Gwamna tazarce

"Sarauniya Joyce Lekan Balogun, matar Olubadan na kasar Ibadan, ta karba Musulunci a hannun babban limamin jihar Oyo, Sheikh Abdul Ganiyy Abubakary Agbotomokekere a karamar hukumar Ibadan ta arewa maso gabas.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Lamarin ya faru ne a yayin wata lakca ta watan Ramadan da aka yi a filin sallar idi na Agodi Gate karkashin shugabancin Honarabul Ibraheem Akintayo. A halin yanzu sunan sarauniyar Khadijah Moshood Lekan Balogun," takardar tace.

Hotunan matar basaraken Yarabawa da ta karba Musulunci, ta koma Khadija daga Joyce
Hotunan matar basaraken Yarabawa da ta karba Musulunci, ta koma Khadija daga Joyce. Hoto daga lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Kada wanda ya kusanci matan Alaafin, an killacewa sabon sarki ne, 'Dan gargajiya

A wani labari na daban, ba sabon labari bane idan ance Oba Lamidi Adeyemi lll, Alaafin na Oyo ya mutu bayan shekaru 52 a karagar mulki, da kuma yaduwar batun mutuwarsa musamman a kafafan sada zumuntar zamani.

Oba Adeyemi mai shekaru 83 ya bar gidan duniya a daren Juma'a bayan jinyar da ya sha a asibitin Afe Babalola dake Ado Ekiti.

Kara karanta wannan

Hotuna: Asiwaju Bola Tinubu ya shiga jerin yan Najeriya da suka garzaya aikin Umrah

Sai dai an ce da 'yan Najeriyan da suka hango yin wuff da matan marigayin basarake da su dakata.

Oba Lamidi na matukar kaunar mata, musamman kyawawa masu jini a jika, bai taba boye wannan batun ba. Hotunan basaraken da matan nasa ya yadu a kowacce kafar sada zumuntar zamani.

A tattaunawar da BBC Yoruba tayi da Chief Ifayeki Elebuibon ya bukaci mazan dake hararo matan sarkin da su kara hakuri. A cewarsa, har yanzu matan na takaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng