Shirin Sallah: Masu Kaji Son Koka Game Da Rashin Ciniki a Kaduna

Shirin Sallah: Masu Kaji Son Koka Game Da Rashin Ciniki a Kaduna

  • Masu sana'ar saya da kaji da talotalo da zabi a garin Kaduna sun koka game da rashin ciniki gabanin bikin karamar Sallah
  • Wasu daga cikinsu sun bayyana cewa a halin yanzu babu ciniki sosai amma suna fatan abubuwa na iya canja wa karshen wata idan an samu albashi
  • Daga cikinsu kuma akwai wadanda suka ce mawuyacin halin rayuwa ne da ake ciki a kasar yasa cinikin kajin bai kai na bara ba

Jihar Kaduna - Wasu daga cikin masu sayar da kaji, talo-talo da agwagi a Kaduna sun koka kan rashin cinikin kajin gabanin bikin karamar Sallah na bana.

Masu sayar da kajin sun nuna damuwarsu a hira mabanbanta da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta yi da su a ranar Talata a Kaduna.

Kara karanta wannan

Yajin Aikin ASUU: Jami'ar Jihar Kaduna Ta Umurci Ɗalibai Da Malamai Su Koma Makaranta Bayan Sallah

Sun ce lamarin abin damuwa ne matuka, duk da cewa suna da kyakkyawan fatan ganin canji da zarar ma'aikata sun samu albashin watan Afrilu.

Shirin Sallah: Masu Kaji Son Koka Game Da Rashin Ciniki a Kaduna
'Karamar Sallah: Masu Kaji Son Koka Game Da Rashin Ciniki a Kaduna. Hoto: Fatima Mohammed.
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wakilin NAN wanda ya ziyarci fitacciyar kasuwar sayar da kaji a Kantin Koli a Babban Kasuwar Kaduna ya hangi mutane da dama suna taya kajin.

Masu sayar da kaji a Kaduna sun magantu kan cinikin sallah

Kabiru Yunusa, wani mai sayar da kaji, Kabiru Yunusa, ya shaida wa wakilin NAN cewa duk cewa farashin kajin ba karuwa ya yi ba, babu ciniki a yanzu.

"Ana sayar da kaza tsakanin N2500 zuwa N4000 bisa la'akari da nauyin ta.
"Kaji masu saka kwai kuma tsakanin N1500 zuwa N2000 ne kudinsu, kajin gidan gona (broilers) kuma farashinsu yana kamawa daga N2500 zuwa N4000," a cewar Yunusa.

Kara karanta wannan

Martanin yan Najeriya kan sabuwar wakar sukar gwamnatin Buhari da Rarara ya yi

A bangarensa, Jamilu Abubakar mai sayar da talotalo ya ce ya dan samu cinikin kaji saura na talotalo.

"Talotalo sun fi tsada, ana sayar da madaidaici tsakanin N9000 zuwa N15000.
"Wannan ba sabon abu bane, mutane su kan zo sayayya ko da ranar jajiberin Sallah ne don haka muna dakon zuwansu," in ji shi.

Baya ga kasuwar, wakilin Legit.ng Hausa ya tuntubi wasu da ke sayar da kajin a kasuwar Kawo.

Hajiya Fatima Mohammed, wacce ke sayar da kaji a unguwar Sabon Kawo cewa ta yi ita kam bana alhamdullah, ta ce ta sayar da kusan rabin kajin da ta saka domin bana yawancin masu kiwon kajin ba su yi ba saboda yana yin rayuwa.

Ta ce farashin kajin nata yana kama wa daga N2500 zuwa 4000, kuma tana sa ran kafin ranar Sallah kajin na iya karewa.

"Alhamdullilahi, mutane sun fara sayan kaji babu laifi na sayar da dama kuma ina fatan kafin ranar Sallah za a iya saye su baki daya," in ji ta.

Kara karanta wannan

Farashin kudin jirgin sama ya sake tashi gabannin bikin karamar sallah

Hakazalika, wani mai sayar da kaji a kasuwar Kawo Kaduna mai suna Malam Sani Mohammed ya ce shima ya fara sayar da kajin amma dai b akamar bara ba, yana mai cewar abubuwa sun canja a kasar ta yadda ba kowa zai iya sayan kajin ba.

Amma ya ce yana fatar za a iya samunsauya zuwa karshen wata idan mutane sun karbi albashi.

"Rayuwa ta kara tsada, ba kowa zai iya sayan kaji ba amma muna fatan za a samu sauya bayan an samu albashi a karshen wata," a cewarsa.

Shugaban wurin aiki ya ba na ƙasa da shi da ke tattaki zuwa wurin aiki kyautar mota

A baya, kun ji wani matashi, Walter, ya yi tattakain mil 20 a ranar sa ta farko ta zuwa wurin aiki. Motar sa ta samu matsala ana gobe zai fara zuwa aikin hakan ya sa ya yanke wannan shawarar.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Attajirin Duniya, Elon Musk Ya Siya Twitter Kan Kuɗi Dalla Biliyan 44

Kafin safiyar, ya yi kokarin tuntubar abokan sa amma babu alamar zai samu tallafi saboda ya sanar da su a kurarren lokaci kamar yadda Understanding Compassion ta ruwaito.

Daga nan ne ya yanke shawarar fara tattaki tun karfe 12am don isa wurin aikin da wuri. Matashin bai bari rashin abin hawan ya dakatar da shi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164