Za'a yi Tawafi na musamman wa Bola Tinubu a Masallacin Ka'abah don nasara a zabe

Za'a yi Tawafi na musamman wa Bola Tinubu a Masallacin Ka'abah don nasara a zabe

  • Mambobin majalisar dokokin jihar Legas zasu yi tawafi na musamman wa tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu
  • Tawafi, wani ibadah ne da ake gudanarwa ta hanyar zagaye Ka'abah mai girma ana yin addu'o'i.
  • Kaakin majalisar yace zasu yi ibadar ne domin rokon Allah ya baiwa Bola Tinubu nasara a zabe mai zuwa

Makkah - Gabanin zaben shugaban kasan 2023, ranar Alhamis za'ayi tawafi na musamman wa Bola Tinubu, dan takarar kujeran shugaban kasa karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a Masallacin Harami dake Makkah, Saudiyya.

Kakakin majalisar dokokin jihar Legas, Mudashiru Obasa, ne ya bayyana hakan a jawabin da ya saki.

A sanarwar, yace za'a fara tawafin ne gabanin Sallar Azahar misalin karfe 12 na rana, rahoton Premium Times.

Tawafi, wani ibadah ne da ake gudanarwa ta hanyar zagaye Ka'abah mai girma ana yin addu'o'i.

Kara karanta wannan

Sallah: Tinubu ya gwangwaje Musulmai da buhunan shinkafa 3,000 a Nasarawa

Jiga-jigan malamai, yan siyasa, mabiya da masoyan Tinubu yanzu haka suna Makkah don halartan Tawafin.

Za'a yi Tawafi na musamman wa Bola Tinubu a Masallacin Ka'abah don nasara a zabe
Za'a yi Tawafi na musamman wa Bola Tinubu a Masallacin Ka'abah don nasara a zabe Hoto: TSG
Asali: Facebook

Kakakin majalisar Legas, Obasa, ya kara da cewa zasu yi ibadar ne don addu'a wa Tinubu gabanin zaben shugaban kasa na 2023.

Yace:

"Mun zo neman alfarman Allah ne a Albarkansa ga Asiwaju a zabe mai zuwa."
"Muna neman taimakon Allah saboda bamu da karfi ko wani iko sai na Allah. Muna wannan ne don goyon bayan neman shugabancin kasar Asiwaju."

Sallah: Tinubu ya gwangwaje Musulmai da buhunan shinkafa 3,000 a Nasarawa

Yayin da shirin bikin sallah ya karato, tsohon gwamnan Legas, kuma 'dan takarar shugaban kasa a shekarar 2023 karkashin jami'iyyar APC, Bola Tinubu, ya bada kyautar buhunan shinkafa 3,000 ga musulman kwarai a jihar Nasarawa, rahoto jaridar Punch ya bayyana.

Tinubu, yayin bada kyautar buhunan shinkafan a ranar Juma'a a Lafia, ya bukaci wadanda suka samu tagomashin da kada su siyar da shinkafar, amma su yi amfani da ita a kan dalilin da yasa aka basu, inda ya ce an yi hakan ne don rage tsadar rayuwar da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel