Hukumar NDLEA ta garkame dukiyoyin Abba Kyari dake Maiduguri, gidaje 6, Plaza mai shaguna 100

Hukumar NDLEA ta garkame dukiyoyin Abba Kyari dake Maiduguri, gidaje 6, Plaza mai shaguna 100

  • Hukumar NDLEA ta maka jan fenti a manyan dukiyoyin tsohon mataimakin kwamishanan yan sanda, Abba Kyari dake birnin Maiduguri
  • Dukiyoyin sun hada da manyan gidajen guda shida a GRA, da kuma kanti mai shaguna kimanin 100
  • Hukumar na zargin cewa ya sayi wadannan dukiyoyin ne da kudin safarar kwayoyin da yake yi

Hukumar hana ta'amuni da safarar muggan kwayoyi a Najeriya a ranar Litinin ta garkame gidaje shida da Plaza daya na tsohon kwamandan IRT, DCP Abba Kyari, dake Maiduguri don bincike.

Plaza mai tsauni biyu, Assurance Plaza, na titin Giwa Barracks kuma yana da shaguna 100.

Sauran gidajen shida dake Maiduguri GRA da ake zargin na dakataccen dan sanda Abba Kyari ne su ma an danna musu jan fenti, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Za'a yi Tawafi na musamman wa Bola Tinubu a Masallacin Ka'abah don nasara a zabe

Abba Kyari
Hukumar NDLEA ta garkame dukiyoyin Abba Kyari dake Maiduguri, gidaje 6, Plaza mai shaguna 100 Hoto: Abba Kyari
Asali: Facebook

NDLEA ta kama attajirin da ya kulla harkallar kwaya da Abba Kyari ta N3bn

Hukumar NDLEA ta samu nasarar kame Afam Mallinson Emmanuel Ukatu, wani attajirin da ake zargin yana da hannu a harkallar safarar miyagun kwayoyi ta DCP Abba Kyari da tawagarsa.

Sanarwar da NDLEA ta fitar ta bayyana cewa Afam na da hannu dumu-dumu a harkallar shigo da miyagun kwayoyi na N3bn da ke da alaka da Abba Kyari.

Bayan shafe watanni ana sa ido akansa, an kama Mista Ukatu wanda shi ne shugaban Kamfanin Mallinson Group of Companies, a cikin jirgin da zai je Abuja daga filin jirgin saman Legas, Ikeja a ranar Laraba 13 ga Afrilu.

Hukumar ta ce Afam babban mai shigo da miyagun haramtattun kayayyaki ne, wadanda suka hada da kwayoyin Tramadol da dai sauransu.

Kara karanta wannan

Hotuna: Asiwaju Bola Tinubu ya shiga jerin yan Najeriya da suka garzaya aikin Umrah

Asali: Legit.ng

Online view pixel