Duk a cikin aiki ne: Jami'an kwana-kwana sun ceto zakaran da ya fada rijiya
- Jami'an hukumar kwana-kwana sun yi nasarar ceto wani Zakara mai shekara da ya fada a cikin rijiya a unguwar Kwalli da ke birnin jihar Kano
- Kakakin hukumar, Saminu Yusuf Abdullahi, ya bayyana cewa jami'ansu sun ceto Zakaran ne bayan sun samu kirar gaggawa daga mazauna unguwar
- Ya ja hankalin jama’ar jihar da su guji barin rijiyoyi a bude domin gudun faruwar makamancin hakan
Kano - Jami’an hukumar kashe gobara ta Kano ta yi nasarar ceto wani zakara mai shekara daya bayan ya fada wata rijiya a unguwar Kwalli da ke birnin jihar.
Mai magana da yawun hukumar, Saminu Yusuf Abdullahi, shine ya tabbatar da hakan a gari Kano, yana mai cewa sun samu kira daga mazauna unguwar inda suka gaggauta amsa kiran tare da ceto zakaran da ransa, jaridar Aminiya ta rahoto.
Abdullahi ya ce:
“Mun samu kiran gaggawa daga wani mutum mai suna Kamalu Garba da misalin karfe 10:12 na safe, inda ya sanar da mu afkuwar lamarin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Nan da nan jami’anmu suka isa wajen, sai suka tarar da wani zakara mai kimanin shekara daya ya fada a rijiya. Daga baya mun yi nasarar ceto shi cikin koshin lafiya.”
Rahoton ya kuma bayyana cewa tuni aka mika zakaran ga mamallakinsa mai suna Abdullahi Umar.
Kakakin hukumar gobarar ya kuma yi kira ga jama’ar jihar da su guji barin rijiyoyi a bude domin gudun faruwar makamancin hakan.
Wani Bawan Allah Mai Shekaru 36 Ya Faɗa Rijiya Ya Mutu a Kano
A wani labarin, wani mutum mai shekaru 36, mai suna Nuhu Rabiu, a ranar Talata ya rasu a Kano jim kadan bayan an ciro shi daga wata rijiya da ya fada ciki, kamar yadda The Punch ta rahoto.
Da ya ke tabbatar da afkuwar lamarin, mai magana da yawun hukumar kwana-kwana a Kano, Saminu Yusif Abdullahi, ya ce a sume aka ciro mutumin daga bisani ya rasu.
Ya ce wani Garba Ali ne ya kira su ya sanar da faruwar abin daga nan kuma suka tura jami'ai cikin gaggawa.
Asali: Legit.ng