Bikin Sallah: 'Yan Ta'adda Na Shirin Kai Hari Masallatai Da Wuraren Shaƙatawa, DSS Ta Gargaɗi 'Yan Najeriya

Bikin Sallah: 'Yan Ta'adda Na Shirin Kai Hari Masallatai Da Wuraren Shaƙatawa, DSS Ta Gargaɗi 'Yan Najeriya

  • Hukumar Yan Sandan Farar Hula, DSS, ta ankarar da yan Najeriya kan wata makirci da wasu bata gari ke shirin aikatawa yayin bukukuwan sallah da bayan sallah
  • SSS din ta ce ta gano cewa wasu miyagu suna hadin gwiwa domin saka bama-bamai a wuraren ibada, wuraren shakatawa da wasu gine-gine masu muhimmanci yayin bikin sallah
  • Don haka hukumar ta bukaci masu wuraren da al'umma ke taruwa su kara taka tsantsan don samar da tsaro yayin da ita kuma da sauran hukumomin tsaro za su dauki matakan dakile harin

Hukumar Yan Sandan Farar Hula, SSS, ta ce ta gano wani shiri da wasu bata gari ke yi na kai hare-hare a muhimman gine-gine, wuraren ibada da wuraren shakatawa musamman yayin bukukuwan sallar da bayan sallah.

Kara karanta wannan

ICPC ta fallasa dabarar da ‘Yan Majalisa su ke yi, su na yin awon gaba da dukiyar talakawa

Kakakin SSS Peter Afunanya, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ƙara da cewa bata garin na neman mayar da kasar tambar kafin 2015 lokacin da aka saka bama-bamai a wasu wurare a kasar, rahoton The Nation.

Bikin Sallah: 'Yan Ta'adda Na Shirin Kai Hari Masallatai Da Wuraren Shaƙatawa, DSS Ta Gargaɗi 'Yan Najeriya
'Yan Ta'adda Na Shirin Kai Hari Masallatai Da Wuraren Shaƙatawa Yayin Bukukuwan Sallah, DSS Ta Gargaɗi 'Yan Najeriya. Hoto: Daily Nigerian.
Asali: UGC

Wani bangare na sanarwar ta ce:

"Duk da cewa an samu rahoton afkuwar abubuwan kamar hakan a wasu sassan kasar, hukumar ta gano shirin da wasu bata gari ke yi na hadin gwiwa don kai hare-hare kan wasu muhimman gine-gine wuraren da mutane ke taruwa kamar wurin ibada da wuraren shakatawa musamman lokacin bikin sallah da bayan sallah.
"Niyyarsu shine cimma wata burinsu da kuma saka tsoro a zukatan yan kasa.
"Don haka hukumar na kira ga mutane da suka mallaki wuraren da su yi takatsantsan don kare afkuwar hakan su tanadi matakan tsaro."

Kara karanta wannan

Martanin yan Najeriya kan sabuwar wakar sukar gwamnatin Buhari da Rarara ya yi

Hukumar ta SSS ta ce ba za ta yi kasa gwiwa ba domin ganin ta samar da tsaro ta hanyar hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro don tabbatar da cewa mutane sun cigaba da rayuwa ciki lumana.

Ta kuma shawarci al'ummar kasa su cigaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum kamar yadda suka saba.

'Yan Sanda Sun Cafke Matashin Da Ke Kai Wa 'Yan Bindigan Neja Abinci

A wani rahoton, Rundunar ‘yan sandan Jihar Neja ta kama wani matashi mai shekaru 20, Umar Dauda wanda ake zargin yana kai wa ‘yan ta’adda kayan abinci a jihar, The Punch ta ruwaito.

A wata takarda wacce jami’in hulda da jama’an rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun ya sanya wa hannu, an samu bayani akan yadda aka kama matashin bayan mazauna yankin sun bayar da bayanan sirri ga hukuma.

Kamar yadda takardar tazo:

“An yi kamen ne a ranar 16 ga watan Maris din 2022, da misalin karfe 11 na dare bayan samun bayanan sirri akan yadda ake yawan ganin wani mai kai wa ‘yan ta’adda kayan abinci a kauyen Kapako da ke Lapai.”

Kara karanta wannan

Karfin hali: Dan Najeriya ya fusata, ya maka Buhari a kotu saboda gallazawa 'yan Najeriya

Saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164