Ina alfahari da kai: Budurwar marigayi matukin jirgin NAF ta yi wallafa mai karya zuciya

Ina alfahari da kai: Budurwar marigayi matukin jirgin NAF ta yi wallafa mai karya zuciya

  • Budurwar da marigayin matukin jirgin NAF, Flight lieutenant Elijah Haruna Karatu ya shirya rayuwa da ita a matsayin mata tayi wani rubutu akansa mai karya zuciya
  • A wallafar da Matankari Deedee tayi cikin kwanakin nan, ta nuna yadda mutuwar ta girgizata, inda ta ce tana matukar alfahari da shi saboda ya yi mutuwar maza
  • Haka zalika, kanin mahaifin marigayin ya tabbatarwa manema labarai yadda suke tsaka da shirye-shiryen aurensa duk da ba a tsaida takamaimar rana ba

Matankari Deedee, budurwar da marigayin matukin jirgin sojin saman Najeriya (NAF), Flight lieutenant Elijah Haruna Karatu yaso aura, tayi wani rubutu mai taba zuciya a kan shi, LIB ta ruwaito.

Karatu da abokin aikinsa, Flight lieutenant Abubakar Muhammad Akali, sun rasa rayukansu ne sanadiyyar hatsarin jirgin saman 'yan koyo na Super Mushshak a ranar Talata, 19 ga watan Afirilu, a NAF base dake Kaduna.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Sojin Najeriya sun halaka 'yan Boko Haram/ ISWAP 27, sun ceto mata 6

Ina alfahari da kai: Budurwar marigayi matukin jirgin NAF ta yi wallafa mai karya zuciya
Ina alfahari da kai: Budurwar marigayi matukin jirgin NAF ta yi wallafa mai karya zuciya. Hoto daga BBC Pidgin
Asali: Facebook

Kawun marigayin jami'in sojin saman, Alhaji Dauda, ya bayyanawa BBC News Pidgin yadda ake tsaka da shirye-shiryen aurensa duk da ba a riga an saka ranar auren ba.

"Cikin kwanakin nan muka tattauna a kan shirye-shiryen aurensa. Duk da ba mu tsaida rana ba, mun tuntubi iyayen yarinyar, kuma sun amince, amma Ubangiji ya tsara komai," a cewar Dauda.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A tsokacin da tayi, Matankari ta ce tana alfahari da masoyinta.

"Rayuwar da masoyina ya yi. Haruna Elijah Karatu, ita ce yadda sadaukai suka yi. Ka shiga jerin wadanda na bada shaida a kansu. Mun fawwala lamurranmu ga Ubangiji. Tare da yin biyayya. Ina alfahari da kai," Ta rubuta hakan.

A daya daga cikin hotunan da ta wallafa, wacce ta gama jami'ar Usman Danfodiyo ta rubuta: "Ba tare da tsammani ba, wannan hoton na dauke da wani irin mahimmanci. Ka ci tare da mala'iku har zuwa lokacin da zamu sake ganawa"

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan bindiga sun farmaki tawagar dan majalisar tarayya a jihar Filato

Haruna Elijah Karatu: Hotunan matukin jirgi NAF na 2 da ya rasa ransa a hatsarin Kaduna

A wani labari na daban, an gano waye dayan matukin jirgin NAF da ya rasa ransa a hatsarin jirgin dakarun da ya auku a ranar Talata a Kaduna. Hafsan sojan mai suna Lieutenant Haruna Elijah Karatu, ya rasu ne sanadiyyar hatsarin da jirginsu ya tafka a jiya Talata.

Vanguard ta ruwaito cewa, Karatu ya rasa ransa ne yayin hatsarin tare da abokin aikinsa, Abubakar Alkali, 'dan jihar Yobe.

An samu labarin yadda Karatu ya yi kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Sakkwoto da Kwalejin Christ Ambassadors, kafin ya shiga makarantar horar da hafsun sojin Najeriya ta jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags:
Online view pixel