Bidiyon soja kan mimbari yana wa'azi dauke da bindiga a kirjinsa ya janyo cece-kuce
- A wani bidiyo, an ga wani soja sanye da kayan sojoji yana wa'azi a kan mimbari a majami'a, hakan ya jawo cece-kuce a kafafan sada zumuntar zamani
- Duba da bidiyon an ga jami'in tsaron rataye da bindiga a kirjinsa yayin da yake wa'azin cike da shauki, rike da littafin Injila a hannunshi daya
- A ganin wasu 'yan Najeriyan, bai zama dole ba a ce dan soja zai yi wa'azi sai ya rike bindiga, yayin da wasu suka yi amfani da hakan a matsayin abun kwasar nishadi
Wani bidiyo ya janyo cece-kuce inda aka ga wani soja rataye da bindiga a kirjinshi yayin da yake gudanar da wani wa'azi.
A guntun bidiyon da @gossipmilltv suka wallafa, ya nuna yadda jami'in tsaron sanye da kayan sojoji,yake amfani da littafin Injila mai launin ja wajen kwatance, lokacin da ya gabatar da wa'azin a cikin majami'a.
Yayi wa'azi ne a kan 'yaren da Ubangiji ke fahimta a wani wuri da ya yi kama da sansanin sojoji.
Haka zalika, an ga daya daga cikin masu sauraronsa a irin kayan sojojin da yake sanye dasu yayin gabatar da wa'azin.
"Yaren da shi kadai Ubangiji ke fahimta shi ne sakamako. Yaren da shi kadai Ubangiji ke fahimta shi ne adalci.
"Ita kanta shari'a na da nasaba kai tsaye da Ubangijin da yafi kowa. Tana da nasaba mai karfi da shi," ya ce ga masu sauraronsa.
Jama'a sun tofa albarkacin bakinsu
Tsokacin masu amfani da kafafan sada zumuntar zamani:
@_ur_lurd ya ce: "Ubangiji ya wa sojojinmu albarka, ko a lokacin da yake bada kalmar Ubangiji, duk da haka yana sanye da Khaki, na wani karin magana da ya ke cewa Ubangijin soja ita ce bindigarsa."
@resmi&meyakini ta ce: "Ba za ku taba ganin soja rike da bindiga yana wa'azi a kasashen da suka cigaba ba. Ya kamata mu yi kokarin ilimantar da sojojinmu, saboda da yawansu ba su san bambamcin hagu da dama ba."
@mizgrace5 ta ce: "Ba na so in yi dariya, ko shaidan zai ji tsoron tsokanar mutum a irin wannan majami'ar."
@dannyross997 ta ce: "Jaruman fagen fama har suna da lokacin bauta, Ubangiji ya jagoranci dukkan sojojin fadin duniya."
@kish_psil ya ce: "Har yanzu Ubangiji na samar da mazajen asali, ba tare da dubi da aikinka ko sana'arka ba."
Ina alfahari da kai: Budurwar marigayi matukin jirgin NAF ta yi wallafa mai karya zuciya
A wani labari na daban, Matankari Deedee, budurwar da marigayin matukin jirgin sojin saman Najeriya (NAF), Flight lieutenant Elijah Haruna Karatu yaso aura, tayi wani rubutu mai taba zuciya a kan shi, LIB ta ruwaito.
Karatu da abokin aikinsa, Flight lieutenant Abubakar Muhammad Akali, sun rasa rayukansu ne sanadiyyar hatsarin jirgin saman 'yan koyo na Super Mushshak a ranar Talata, 19 ga watan Afirilu, a NAF base dake Kaduna.
Asali: Legit.ng