Sarkin Oyo ya hango mutuwarsa, ya fada mana cewa magabatansa sun yi kira - Hadimarsa
- Wata hadima a fadar sarkin Oyo ta bayyana cewa marigayi Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi III, ya yi hasashen mutuwarsa
- Babban basaraken dai ya rasu ne a daren ranar Juma’a a asibitin koyarwa na jami’ar Afe Babalola da ke Ado-Ekiti
- A cewar hadimar, kimanin makonni biyu da suka gabata sarkin ya kira su sannan ya sanar da su cewa magabantansa sun ce ya zo
Oyo - Wata hadima a masarautar Oyo ta yi ikirarin Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi III, ya yi hasashen mutuwarsa tun kan ta zo.
Ta bayyana hakan ne yayin da take zantawa da manema labarai a fadar sarkin Oyo a ranar Asabar, 23 ga watan Afrilu, jaridar Punch ta rahoto.
Babban basaraken kasar Yarbawan ya rasu a daren ranar Juma’a, 22 ga watan Afrilu, a asibitin koyarwa na jami’ar Afe Babalola.
Ma’aikaciyar fadar ta bayyana cewa basaraken ya riga ya yi hasashen mutuwarsa ne a yan makonnin da suka gabata.
Ta bukaci mutane da su samu nutsuwar zuciya kasancewar marigayin ya yi ingantacciyar rayuwa.
Ta ce:
“Mahaifina ya je don ya sadu da magabatansa. Alaafin ya je yin wasa da magabatansa ne. Bai mutu ba.
“Makonni biyu da suka gabata, ya kiramu sannan ya fada mana cewa marigayi mahaifinsa na kiransa da ya zo. Mun tsorata sannan muka tambaye shi idan da gaske ya ga mahaifinsa.
“Ya hau karagar mulki yana da kuruciya kuma ya kasance mai arziki sannan Allah ya albarkace shi da tsawon rai, ya kiyaye kujerar, ya daukaka al’adun Yarabawa kuma ya kasance abin koyi na sarauta. Mun yi farin cikin samun shi a matsayin sarki.”
Limamin Kasar Oyo ya ja Sallar jana'izar Oba Lamidi Adeyemi
A gefe guda, mun kawo a baya cewa Babban Limani kasar Oyo, Sheikh Mas'ud Ajokidero, da dimbin jama'a sun yi wa marigayi Oba Lamidi Adeyemi Sallar jana'iza a fadarsa dake cikin jihar Oyo.
Hotunan da Legit ta samu daga wani Kehinde sun nuna lokacin da jama'ar garin ke kabarta Sallah kan gawar.
Asali: Legit.ng