Gwamnatin Saudiyya ta baiwa Najeriya kujeran Hajji 43,000 bana

Gwamnatin Saudiyya ta baiwa Najeriya kujeran Hajji 43,000 bana

  • Sabanin kujeru 96,000 da Najeriya ke samu a baya, Saudiya ta bada kujeru 43,000 ga maniyyata daga Najeriya
  • Duk da cewa hukumar NAHCON da kanta bata sanar da hakan ba, majiyoyi sun tabbatar da hakan
  • Shekaru biyu baya yanzu maniyyata daga Najeriya basu samu daman gudanar da ibadar Hajji

Abuja - Gwamnatin kasar Saudiyya ta baiwa Najeriya kujerun Hajji 43,000 a shirin ibadar Hajjin da za'a yi bana 2022.

Daily Trust ta ruwaito cewa majiyoyi daga cikin hukumar alhazai ta kasa NAHCON sun ce nan ba da dadewa ba hukumar zata sanarwa yan Najeriya.

Legit ta tuntubi daya daga cikin kwamishanonin hukumar NAHCON wanda ya tabbatar da cewa lallai an baiwa Najeriya kujeru sama da 40,000 bana amma ya bukaci mu sakaye sunansa.

Yace:

"Wasu abokai na biyu a ma'aikatar hajji da Umrah dake Saudiyya ya tabbatar min cewa Najeriya ta samu sama da kujeru 40,000."

Kara karanta wannan

Karin bayani: Jirgin saman sojoji ya hatsari a Kaduna, jami'ai 2 sun mutu

"Amma mu a NAHCON mun shirya tafiyar da yan Najeriya 50,000 a ganawar da muka yi."

Gwamnatin Saudiyya ta baiwa Najeriya kujeran Hajji 43,000 bana
Gwamnatin Saudiyya ta baiwa Najeriya kujeran Hajji 43,000 bana
Asali: Facebook

Sama da yan Najeriya 150,000 yanzu haka da suka biya kudi na kyautata zaton samun halartan hajji.

Rabon da yan Najeriya su halarci aikin Hajji tun shekarar 2019.

A shekarar 2020 da 2021, kasar Saudiyya bata baiwa yan Najeriya da wasu kasashen duniya damar zuwa ba sakamakon bullar annobar Korona da ta addabi duniya.

NAHCON: Adadin gurbin da muke sa ran Saudiyya zata baiwa Najeriya a Hajjin bana

Kasar Saudiyya ta cire duk wani takunkumi a Harami, Najeriya na ci gaba da shirin tunkarar aikin Hajjin bana.

A Hajjin bana, Najeriya na sa ran samun izini daga kasar Saudiyya na tura mahajja sama da 47,500.

Kara karanta wannan

Nisan kwana: Dan takarar kujerar majalisar jiha ya tsallake rijiya da baya a harin 'yan bindiga

Sabanin shekarun baya da Najeriya ke samun adadin mahajjata da suka kai akalla 95,000, a wannan shekarar Najeriya na sa ran Saudiyya ta ba da 50% na adadin mahajjata da aka saba.

Hasashen adadin ya ne daga bakin kwamishinan tsare-tsare, bincike, kididdiga da yada labarai na hukumar Hajji ta kasa (NAHCON), Sheikh Prince Suleman Momoh a yayin wata hira da wakilinmu na Legit.ng Hausa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel