Yanzun nan: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin wasu jiga-jigai daga masana'antar Dangote

Yanzun nan: Shugaba Buhari ya karbi bakuncin wasu jiga-jigai daga masana'antar Dangote

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin wasu jiga-jigai daga masana'antar Dangote
  • Wannan ziyara tasu ta zo ne bayan da shugaban ya gana da wasu jiga-jigan gwamnati a jiya Alhamis
  • Hotunan da fadar shugaban kasa ta fitar sun nuna lokacin da shugaban kasa ke karbar lambar yabo daga jami'an

Fadar shugaban kasa, Abuja - A yau ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da wasu jiga-jigai daga rukunin masa'anatun Dangote a fadarsa da ke Abuja.

Legit.ng Hausa ta samo labarin ne yayin da hadimin shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Buhari Sallau ya yada wasu hotuna na ganawar ta shafinsa na Twitter.

Hotunan ganawar Buhari da jama'ar Dangote
Yanzun nan: Shugaba Buhari ya gana da jiga-jigai daga masana'antar Dangote | Hoto: @Buharisallau1
Asali: Twitter

Hotunan da ya yada suna dauke da rubutu kamar haka:

"Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin kwamitin gudanarwa ta rukunin masana'antun Dangote a fadar shugaban kasa a yau Laraba 22 ga watan Afrilu 2022."

Kara karanta wannan

2023: Kwana Kaɗan Bayan Buhari Ya Musu Afuwa, An Yi Kira Ga Dariye Da Nyame Su Fito Takarar Shugaban Ƙasa

Ya zuwa yanzu dai ba a san dalilin ganawar tasu ba, duk da cewa sanarwar ta ce shugaban ya karbi bakuncinsu ne a wata ziyara da suka kawo masa.

Sai dai, hotunan sun nuna cewa, jami'an daga Dangote sun mika wa shugaban kasa Muhammadu Buhari lambar yabo ta kokarinsa.

Hoton da ke jikin allon lambar yabon ya nuna lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari na bude wasu ayyuka a ranar 22 ga watan Maris na 2022.

idan baku manta ba, mun kawo muku rahoto a baya cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wasu ayyuka a jihar Legas, ciki har da masana'antar taki ta Dangote.

Wannan ganawa ta shugaba Buhari da jama'ar Dangote ta zo ne kwana guda bayan da shugaban ya gana tare da tattaunawa da jiga-jigan gwamnatinsa a jiya Alhamis, 21 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Abin da Shugaban kasa ya fadawa Malamai da Sarakuna da suka yi buda-baki a Aso Villa

Kalli hotunan ganawar:

Shugaba Buhari ya gana da hafsoshin tsaro, ministoci kan batun tsaron Najeriya

A wani labarin, labarin da Legit.ng Hausa ke samu daga fadar shugaban kasa ya bayyana cewa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jagorantar wata ganawa da wasu ministoci da shugabannin hukumomin tsaro a fadarsa da ke Abuja.

Taron wanda aka fara shi da misalin karfe 10 na safe, ya biyo bayan shawarwarin da majalisar dokokin kasar ta bayar ne kan duba lamarin rashin tsaro a fadin kasar.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo; Sakataren Gwamnatin Tarayya; Boss Mustapha; Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari; da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Manjo Janar Babagana Monguno (rtd.) sun halarci taron.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.