Karin bayani: Gidaje da shaguna sun kone yayin da tankar mai ta fadi ta fashe a Legas
- Fashewar tankar mai da ya afku a jihar Legas a yau din nan ta haifar da fargaba da firgici a tsakanin mazauna garin yayin da aka ce mutum guda ya mutu
- Lamarin da ya faru ne da sanyin safiyar Juma’a, 22 ga watan Afrilu, a unguwar Alagbodo, daura da babbar hanyar Legas zuwa Abeokuta
- A halin da ake ciki, gobarar wadda Daraktar hukumar kashe gobara ta Legas, Margret Adeseye ta tabbatar, ta yi sanadiyar lalata shaguna a yankin tare da lalata kayayyaki ciki har da gidaje
Jihar Legas - Akalla mutum daya ne aka tabbatar da mutuwarsa yayin da gidaje da shaguna suka kone bayan da wata tankar mai dauke da man fetur ta fashe a Ajegunle Bus-stop, Alagbado, daura da babbar hanyar Legas zuwa Abeokuta da sanyin safiyar Juma’a, 22 ga watan Afrilu.
Hukumar kashe gobara ta jihar Legas a halin yanzu tana kan yakar gobarar da ta barke a Titin Toll Gate Bus Stop, babban titin Abeokuta, mai iyaka da jihohin Legas da Ogun, Vanguard ta ruwaito.
An tattaro cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe 2 na dare yayin da wasu bata gari ke diban mai daga tankar da ta fadi, inji rahoton Daily Trust.
Daraktar hukumar kashe gobara ta Legas, Margret Adeseye, a lokacin da take bayar da karin haske ta ce an gano mutum daya da ya mutu a gobarar da kuma motoci uku da suka kone.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ta ce:
“Sai dai ma’aikatan kashe gobara na Agege, Ikeja da Alausa ta Jihar Legas ne suka shawo kan lamarin tare da yin amfani da dabarar kashe gobara na sinadarin kumfa don dakile gobarar.
“An kuma tabbatar wa da jama’a cewa an shawo kan lamarin yayin da ake ci gaba da gudanar da aikin kwashe sauran tarkacen gobarar.
"Sai dai su yi taka-tsan-tsan tare da kamewa saboda an karkatar da zirga-zirgar ababen hawa masu fita daga Legas don gogayya da ababan hawa masu shigowa."
Bidiyon yadda fasinja ta yanke jiki ta fadi, tace ga garinku a filin jirgin sama dake Abuja
A wani labarin, wata fasinjar jirgin sama, wacce aka fi sa ni da Mama Tobi ta yanke jiki ta fadi inda ta mutu a ranar Laraba, 20 ga watan Afirilu a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja, The Nation ta ruwaito.
Kamar yadda jaridar ta bayyana, wani lauya mai suna Che Oyinatumba ne ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Ganau din ya wallafa bidiyoyin a shafinsa na Facebook, inda ya nuna yadda lamarin ya auku. Kamar yadda bidiyon ke nunawa, an ga wasu fasinjoji na yi wa matar da ba a san ko wacece ba addu'o'i bayan ta yanke jiki ta fadi.
Asali: Legit.ng