Bidiyo: Bayan shekara 20 da batan ta, mahaifiyar yara 8 ta dawo gida da kafafunta

Bidiyo: Bayan shekara 20 da batan ta, mahaifiyar yara 8 ta dawo gida da kafafunta

  • Daga karshe an gano wata mata mahaifiyar 'ya'ya takwas mai shekaru 68, mai suna Florence Ikhine da ta bace a Benin dake jihar Edo a 2002
  • Bayan kwashe shekaru 20, an ganta ba tare da tsammani ba a ranar 20 ga watan Afirilu, 2022 wuraren layin Eharkpen, cikin babban birnin Benin
  • Florence wacce 'ya'yanta duk sun yi aure ta samu tarba daga danginta cike da hawayen farinciki da mamakin dawowarta bayan yanke kauna daga sake ganawa da ita

Edo - Wasu 'ya'ya sun tsunduma cikin tsananin farinciki bayan an gano mahaifiyarsu Florence Ikhine, wacce ta bace a shekarar 2002 a Benin dake jihar Edo bayan kwashe shekaru 20 da bacewarta.

Princess Ehima Elema wacce ta sanar a shafinta na Facebook a shekarar 2019 cewa Florence, mahaifiyar yara takwas ta bace, ta sanar da dawowar mahaifiyar 'ya'ya takwas din.

Kara karanta wannan

Kyawawan hotuna 8 na fitacciyar 'yar kwalisa, tauraruwa Zari Hassan sanye da hijab a Ramadan

Bidiyo: Bayan shekara 20 da batan ta, mahaifiyar yara 8 ta dawo gida da kafafunta
Bidiyo: Bayan shekara 20 da batan ta, mahaifiyar yara 8 ta dawo gida da kafafunta. Hoto daga Ehima Elema
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Princess ta ruwaito yadda aka gano dattijuwar mai shekaru 68 a ranar Laraba, 20 ga watan Afirilu, 2022 wuraren titin Ehaekpen a Benin City dake Edo, inda daya daga cikin 'ya'yanta ke zama.

Legit.ng sun tattaro cewa duk 'ya'yanta maza da mata sun yi aure yanzu.

Haka zalika, Princess ta wallafa wani bidiyon da ke bayyana yadda iyalin Florence suka sha kuka bayan dawowarta ba tare da tsammani ba.

Yayin tsokaci tare da hada wallafar bacewar matar da tayi a 2002 ta rubuta: "Babu abunda ya gagari Ubangiji.
"Mahaifiyar kawata ta dawo gida bayan shekaru 20 da aka sanar da bacewarta"

A shekarar 2019 nayi wallafa don taimakawa wajen sanin inda take a lokacin da 'ya'yan, musamman kawata suke tsaka da nemanta. Wanda ya sake daukar wasu shekaru uku bayan tsananin binciken inda take kafin a yi nasarar ganinta.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Ofishin Babban Bankin Najeriya, CBN, Ta Kama Da Wuta

"Ba zaku gane irin farincikin da suka shiga ba."

'Yan Najeriya sun yi martani:

Eddie peters ta ce:

"Ba bacewa tayi ba, barin gida tayi, gami da yin watsi da 'ya'yanta. Ba gidan yari aka ka ita ba, to me ya tsaida ta na tsawon shekaru 20?"
Ju Dith ta ce: "Na taya su murna! Amma me ye karin bayani a kan hakan? Meya faru da ita?"
Chika Omuzaga ya ce: "Ubangiji ya yi abu mai kyau, ya cancanci godiya, Ubangiji daya. "Mun gode maka Jesus "
Osarode Iduoriyekemwen ya ce: "Ya a kai ta iya gano 'ya'yanta? Wa ya taimaka mata wurin nemo su! Ya maganar saka 'yan sanda don bincikar yadda "ta sake bayyana ba tare da tsammani ba"?

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng