Zamfara: Bayan Raba Wa Sarakuna Cadillac, Matawalle Ya Tura Malamai 97 Umrah Don Yin Addu'a Kan 'Yan Bindiga
- Gwamnatin Jihar Zamfara ta tura malamai 97 na addinin musulunci kasar Saudi Arabia don yin Umrah a ranar Laraba musamman don kawo karshen ta’addanci a jihar
- Wannan daya ne daga cikin matakan da gwamnatin ta dauka na dawo da zaman lafiya da tsaro jihar kamar yadda mataimakin gwamnan jihar, Hassan Nasiha ya nuna
- Nasiha, yayin yi wa malaman jawabi kafin su wuce ya ce kada su manta, su hada da sauran matsalolin da Najeriya ta ke ciki a cikin addu’o’insu
Zamfara - A ranar Laraba, Gwamnatin Jihar Zamfara ta tura malaman addinin musulunci 97 zuwa kasa mai tsarki don yin Umrah musamman domin addu’o’i akan kawo karshen ta’addanci a jihar, rahoton Daily Trust.
A cikin matakan da gwamnatin ta dauka wurin dawo da tsaro da zaman lafiya a jihar shi ne tura malaman Saudi Arabia don yin addu’a a watan Ramadana mai tsarki.
Ana sa ran za su ziyarci wurare masu daraja da tsarki a garin Makkah da Madina da niyya ta musamman ta yi wa Najeriya gaba daya addu’o’in na dawowar zaman lafiya mai dorewa.
Yayin jawabi ga malaman kafin su wuce, Hassan Nasiha, mataimakin gwamnan jihar ya ce kada su manta da jiharsu da mutanensu a addu’o’insu.
An nemi su dage akan addu’o’i ga jiharsu musamman idan su ka duba su aka wakilta a maimakon miliyoyin mutane
Nasiha ya nemi su yi addu’o’in da fatan Ubangiji zai kawo karshen matsalolin Najeriya.
Daily Nigerian ta bayyana yadda wani malami, Atiku Balarabe, yayin jawabi ga malaman ya bukaci su kasance masu mayar da hankali akan ibada da addu’o’i idan sun isa Saudi Arabia.
Ya ce kada su manta da cewa su aka wakilta a maimakon miliyoyin sauran ‘yan jihar don su nemi Ubangiji ya kawo karshen ta’addanci da sauran matsalolin da jihar ta ke fuskanta.
A farkon wannan watan, Zamfara ta rarraba tsadaddun motoci fiye da 200 ga shugabannin gargajiyan jihar.
'Yan Ta'addan Da Suka Kai Hari Sansanin Sojoji Na Kaduna Sun Ɗanɗana Kuɗarsu, Lai Mohammed
A bangare gudan, Gwamnatin Tarayya, a ranar Laraba ta ce yan ta'addan da suka kai hari sansanin sojoji da ke Birnin Gwari a Kaduna sun sha azaba a hannun sojoji a yayin da suka fatattake su, rahoton Daily Trust.
Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke amsa tambayoyi kan tsaro bayan taron FEC da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a Aso Villa a Abuja.
Rahotanni sun bayyana cewa sojoji 11 ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da wasu da dama suka jikkata yayin harin na ranar Talata.
Asali: Legit.ng