Buhari: Mutane Suna Da Manta Alheri, Munyi Aiki Sosai Duk Da Cewa Babu Isasshen Kuɗi a Hannun Mu

Buhari: Mutane Suna Da Manta Alheri, Munyi Aiki Sosai Duk Da Cewa Babu Isasshen Kuɗi a Hannun Mu

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce mulkinsa ya yi wa Najeriya kokari kwarai duk da karancin kayan aikin da ke hannunsu
  • Shugaban Buhari ya bayyana hakan ne a taron Kwamitin Gudanarwa ta Kasa, NEC ta jam’iyyar APC wanda aka yi a Abuja ranar Laraba
  • Ya ce ya hau mulki a lokacin ‘yan ta’adda su na shugabantar wasu kananun hukumomi, yayin da Kudu-Kudu ta ke a rikice, amma yanzu su na cikin zaman lafiya

Abuja - Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana irin kokarin da gwamnatinsa ta yi duk da kasancewar babu isassun kayan aiki a hannu, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaba Buhari ya yi wannan furucin ne ranar Laraba yayin da ake taron Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar APC ta kasa, NEC, wanda aka yi a garin Abuja.

Kara karanta wannan

Buhari ga shugabannin APC: Ku haramtawa PDP mulki a 2023 kamar yadda kuka yi a 2015

Buhari: Mutane Suna Da Manta Alheri, Munyi Aiki Sosai Da Ƙanƙanin Kuɗin Da Muke Da Shi
Mun yi kokari sosai duk da karancin kayan aikin da ke hannu, mutane suna da manta alheri ne, Buhari. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Ya ce ya fara mulki ne lokacin ‘yan ta’adda sun mamaye wasu kananun hukumomi suna shugabantarsu da kuma Kudu-Kudu, wadanda a yanzu haka su ke zaune cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Buhari ya ce mutane suna da mantuwa

A cewar Buhari bisa ruwayar NewsWireNGR:

“Ina so ku tuna halin da muka tsinci kasar nan yayin da muka hau mulki. Kananun hukumomi nawa na Arewa maso Gabas ne a lokacin su ke karkashin ‘yan ta’adda? A Kudu-Kudu kuwa, mun san halin da su ke ciki; amma yanzu suna zaune a zaman lafiya.
“Mutane su na da mantuwa. Babbar matsalar mu a yanzu yankin Arewa maso Yamma da kuma Arewa Tsakiya ne. Mutane su na ta halaka junayensu a yankunan, yanzu za mu dage kwarai akansu.”

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari tayi magana a kan ceto Bayin Allah da aka sace a jirgin Kaduna-Abuja

Shugaban kasa ya ja kunnen mutane akan danniya a jam’iyya mai mulki, inda ya ce a bi hanyoyin da suka dace wurin samun kujeru. Ya hori ‘yan jam’iyyar da su kasance masu kauce wa rashawa.

Ya ci gaba da cewa:

“Rashin bin hanyoyin da suka dace sun janyo mana asarar wasu kujerun. A baya wasu manya a jam’iyyarmu sun bar ta zuwa wata saboda yadda wasu shugabannin jam’iyyar suka yi musu danniya.
“Ina mai jan kunne, don hakan na iya janyo fadan cikin jam’iyya. Muna kuma son mu ci nasara don haka mu hade kawunanmu iya wuya.”

Shugaban kasa ya shawarci ‘yan APC da su kiyaye aikata irin abinda ya sa PDP ta fadi a zaben 2015

Shugaban kasar ya sanar da sabbin shugabannin Kwamitin Ayyuka ta Kasa, NWC wadanda NEC ta nada na wucin-gadi, da su yi iyakar kokarinsu wurin hade kan ‘yan jam’iyyar ta hanyar bayar da dama ga mutane don kowa ya bayyana ra’ayinsa.

Dangane da babban zabe mai zuwa na 2023, Buhari ya bukaci ‘yan jam’iyyar da su kiyaye yin abubuwan da su ka janyo har PDP ta fadi a zaben 2015.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164