Buhari ya yi buda baki da gwamnoni, shugabannin tsaro da sauransu
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gayyaci gwamnonin jihohi 36 zuwa fadar shugaban kasa domin yin buda bakin azumin Ramadana
- Daga cikin wadanda aka gayyata fadar villa harda manya hafsan tsaro na kasar da shugabannin kungiyoyin tsaro
- Kafin zaman cin abincin wanda aka yi a ranar Talata, 19 ga watan Afrilu, wasu daga cikin bakin sun yi sallar Magriba tare da Buhari a masallacin Aso Rock
Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin gwamnonin jihohi 36 zuwa taron buda baki a fadar shugaban kasa, Abuja a ranar Talata, 19 ga watan Afrilu.
Har ila yau, daga cikin wadanda shugaban kasar ya gayyata taron buda bakin harda manyan hafsoshin tsaro na kasar da wasu manyan jami'an gwamnati.
Wasu daga cikin mutanen da aka gayyata sun yi sallar Magrib tare da shugaban kasar a masallacin fadar shugaban kasa kafin aka fara taron buda bakin.
2023: A Manta Da Batun Zaɓe Bayan Saukan Buhari, a Kafa Gwamnatin Wucin Gadi Da Za Ta Saita Najeriya, Dattijon Ƙasa Ya Bada Shawara
Kamar yadda hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na Facebook, an gudanar da taron ne a dakin taro na Banquet Hall, da ke fadar shugaban kasa, Abuja.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Shugaban kasar ya yi taron buda baki da shugabancin bangaren shari’a na kasa a ranar Alhamis.
A wajen taron, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauki alkawarin cewa bangaren zartarwa za ta ci gaba da mutunta bangaren shari’a bisa iyakokin da kundin tsarin mulkin kasar ya shimfida domin karfafa damokradiyyar kasar, rahoton Daily Nigerian.
2023: Hadimin Shugaban Kasa ya koma gida, zai shiga takarar ‘Dan Majalisa a Kano
A wani labarin, mai taimakawa shugaba Muhammadu Buhari a kafofin sada zumunta na zamani, Bashir Ahmaad ya na shirin takarar ‘dan majalisa a zaben 2023.
Malam Bashir Ahmaad ya bayyana haka a shafinsa na Facebook a ranar Talata. Ahmaad zai nemi kujerar Gaya/Ajingi/Albasu a majalisar wakilan tarayya.
Da yake bayani a shafin na sa, hadimin shugaban kasar ya tabbatar da cewa ya ziyarci mahaifarsa watau Gaya da ke wajen birnin Kano a cikin makon nan.
Asali: Legit.ng