Kano: Rundunar Ƴan Sanda Ta Biya Ɗan Adaidaita Sahu Miliyan 3 Saboda Cin Zarafinsa Yayin Da Ya Ke Bakin Aiki

Kano: Rundunar Ƴan Sanda Ta Biya Ɗan Adaidaita Sahu Miliyan 3 Saboda Cin Zarafinsa Yayin Da Ya Ke Bakin Aiki

  • Hukumar Dauka da Ladabtar da Yan Sanda, PSC, ta biya wani mai adaidaita sahu, Dayyabu Auwalu, diyyar N3m a Kano
  • Hakan ya biyo bayan karar da ya shigar ne a babban kotun tarayya da ke Kano kan azabatar da shi da yan sandan suka yi a yayin da ya ke aikinsa
  • Barista Abba Hikima, lauyan Auwalu, ya tabbatar da lamarin a shafinsa na Facebook yana mai cewa yana fatan hakan zai zama darasi ga saura

Jihar Kano - Hukumar Dauka da Ladabtar da Yan Sanda, PSC, ta biya wani mai sana'ar adaidaita sahu a Jihar Kano, Dayyabu Auwalu, diyyar Naira miliyan 3.

Daily Trust ta rahoto cewa hakan ya biyo bayan umurnin da Babban Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta bada, bayan wasu yan sanda sun lakada masa duka, yayin da ya ke aikinsa.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Jirgin saman sojoji ya hatsari a Kaduna, jami'ai 2 sun mutu

Kano: Rundunar Ƴan Sanda Ta Biya Ɗan Adaidaita Sahu N3m Saboda Azabtar Da Shi Ba Tare Da Hakki Ba
Kano: Rundunar Ƴan Sanda Ta Biya Ɗan Adaidaita Sahu N3m Saboda Lakada Masa Duka Ba Tare Da Hakkin Doka Ba. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Jami'an yan sandan da aka samu da laifin sun hada da Abdullahi Daura da tsohon DPO na ofishin yan sanda da ke Kuntau a Kano, CSP Abdullahi.

Muna fatan hukuncin zai zama darasi ga sauran yan sanda, Lauyan Dayyabu, Barista Abba Hikima

Da ya ke sanar da lamarin a shafinsa na Facebook, lauyan Auwalu, Barista Abba Hikima ya ce:

"Ana fatan wannan zai zama izinina ga wasu yan sandan da ke musgunawa al'umman gari, da kuma ita hukumar kanta."

Kaduna: Lauya Ya Yi Ƙarar Wani Mutum a Kotun Shari'a Saboda Ƙin Biyansa N100,000 Kuɗin Aikinsa

A wani rahoton, wata kamfanin lauyoyi a Kaduna mai suna Moonlight Attorneys, a ranar Litinin, ta yi karar wani Yusha'u Abdullahi a kotun shari'a saboda kin biyan kudin N100,000 kudin aikin da suka masa.

Kara karanta wannan

Nisan kwana: Dan takarar kujerar majalisar jiha ya tsallake rijiya da baya a harin 'yan bindiga

Lauyan wanda ya shigar da karar, Atiku Abdulra'uf, ya bayyana cewa wanda aka yi karar ya nemi wanda ya shigar da karar ya yi masa aiki, kuma suka amince zai biya adadin a matsayin kudin aiki, rahoton Daily Nigerian.

Ya yi bayanin cewa bayan an kammala aikin, wanda aka yi karar ya ki biyan kudin duk da yarjejeniya da suka yi, hakan yasa wanda ya shigar da karar ya taho kotu don a bi masa hakkinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164