Daga cakwalkwali zuwa makaranta: Yadda Ahmed Musa ya tallafi yaro da danginsa a Legas
- Dan kwallon Najeriya Ahmed Musa ya sha yabo a shafukan sada zumunta saboda sanya murmushi a fuskar wani yaro da ke zaune a wata unguwar talakawa a jihar Legas
- Matashin dan shekaru 30 da haihuwa da ya shahara ne saboda ayyukan jin kai, ya tura jama'arsa su ziyarci gidansu yaron da rigarsa daga bisani kuma ya sanya shi a makaranta
- Musa ya yada wani faifan bidiyo mai ban sha'awa da ke nuna lokacin da yaron ya fara karatu tare da wasu yara
Dan wasar kwallon kafa na kungiyar Fatih Karagümrük ta Turkiyya Ahmed Musa ya narka shafukan yanar gizo yayin da ya farantawa dangin wani yaro da ke zaune a wata mummunar unguwa a Legas.
Musa ya taimaki dangin yaron kuma ya hada tallafa masu ta hanyar tura yaron makarantar da ke unguwar da ke fama da ambaliyar ruwa.
An ga dan wasan kwallon kafan na Najeriya a cikin wani faifan bidiyo da aka watsa a shafinsa na Instagram, inda ya yi alkawarin aika kudi ga dangin.
An dauki dan gajeren faifan bidiyon lokacin da mutanen Ahmed Musa suka ziyarci dangin yaron.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya samu rigar Musa ta Super Eagles
A yayin ziyarar sun mika sakon Musa ga dangin yaron tare da mika wa yaron rigar Super Eagles mai dauke da suna da lambar Ahmed Musa.
Faifan ya kuma nuna lokacin da yaron ya fara zuwa makaranta. An ganshi cikin fara'a a lokacin da ya shiga aji cikin kayan makaranta kamar dai sauran yaran tsararrakinsa.
Musa ya yada wannan faifan bidiyon tare da doguwar nasiha game da nuna soyayya ga juna.
Rubutun nasa ya ce:
"Lokuta da dama muna jiran lokacin da muke samu da yawa kafin mu fara taimakawa wasu amma a duniyarmu ta yau, dan karamin taimakonka zai taimaka nesa ba kusa ba.
"Lokacin da muka manta da halin da wasu mutane ke ciki, muna jin kamar duniya tana gaba da mu amma yanayi irin wannan a nan ya kamata ya taimaka mana mu fahimci rayuwa.
"Ba tare da la'akari da kabilarmu ko harshenmu ba, duk daya muke, mu yada soyayya a ko da yaushe domin tare za mu iya samun nasarori masu yawa."
Kalli bidiyon:
Ra'ayoyin jama'a a kafar Instagram
@lapiro.m yace:
"Wa ya san yadda wannan wurin zai kasance idan ana ruwan sama da misalin karfe 2:00 na dare?"
@baba_lingo1 yace:
"Allah ya saka maka da mafificin alherin kauna da soyayya ga masu karamin karfi sanin sarai cewa Allah ya albarkace ka gwargwadon yadda zaka taimaki wasu da tunanin tallafawa wandanda suke cikin birni da lungu da sako, saboda su ma uwa da iyaye ne suka haife su. Alhamdurulah."
@ike_chike yace:
"Gwamnati bata damu ba. Gaskiyar magana kenan... Allah ya saka maka da alheri Ahmed. abin koyi a ko da yaushe."
@jemsy_benz ya ce:
"Alheri ba ya kadan, dan adamtaka ne kan gaba, Allah ya saka maka da bisa daga muryarka."
Matashi ya yi farin cikin kammala Digiri bayan shekara 10 ya na fafatawa a ABU Zaria
A wani labarin, wani Bawan Allah mai suna Abba Abubakar Santalee ya bayyana farin cikinsa yayin da ya kammala karatun digirin farko a jami’ar ABU Zaria.
Legit.ng Hausa ta fahimci Abba Abubakar Santalee ya fito ya bayyana wannan abin alheri ne a shafinsa na Twitter a ranar Talata, 12 ga watan Afrilu 2022.
Inda farin cikin Pharm. Abba Abubakar Santalee yake shi ne, ya dauki lokaci mai tsawo kafin samun takardar shaidar Digiri a wannan babbar jami’a.
Asali: Legit.ng