Shigowar fasahar 5G: Jerin wayoyi masu amfani da 3G da za su daina aiki a 2022

Shigowar fasahar 5G: Jerin wayoyi masu amfani da 3G da za su daina aiki a 2022

Bayan sauya hanyar sadarwa zuwa 5G don samun ingantacciyar hanyar hawa Intanet, musamman ta fuskar sauri, manyan kamfanonin samar da ayyukan wayoyi suna kokarin kawar da wayoyin salula masu amfani da 3G.

Wannan shiri na dakatarwa da ta taso za ta kuma shafi wayoyin da ake amfani da su kawai don kiran wayan 911 ne da wasu tsofaffin wayoyin hannu na 4G da basa amfani da tsarin Voice over LTE (VoLTE ko HD Voice) mai murna rangadadau.

Wannan canjin zai shafi wayoyin hannu kamar IPhone 5, IPhone 5S da Samsung Galaxy S4, da kuma wayoyi masu yawan gaske; farawa daga 2022.

Yadda 5G ta yi sanadiyyar korar 3G a kasuwar duniya
Shigowar fasahar 5G: Jerin wayoyi masu amfani da 3G da za su daina aiki a 2022 | Hoto: nairametrics.com
Asali: Getty Images

A cewar wata sanarwa da Hukumar Sadarwa ta Tarayyar Amurka (FCC) ta fitar, wacce WashintonPost ta gani, ta ce kamfanonin wayar salula za su rufe hanyoyin sadarwarsu a wasu wayoyi a ranaku daban-daban kamar haka:

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Tsohon na kusa da Buhari ya fice daga jam'iyyar APC, ya jero dalilai

  1. AT&T - Fabrairun 2022.
  2. Verizon - 31 ga watan Disamban 2022.
  3. T-Mobile za ta rufe hanyar sadarwar 3G CDMA akan Sprint zuwa Maris 31, 2022
  4. 4G LTE na Sprint - Yuni 30, 2022
  5. Cibiyar sadarwa ta T-Mobile mai 3G UMTS - Yuli 1, 2022

Sauransu kamar Cricket, Boost, Straight Talk, da masu samar da fasahar sadarwa na wayoyin hannu da yawa wadanda ke amfani da hanyoyin sadarwar AT&T, Verizon, da T-Mobile na iya shiga cikin wannan totse.

Me za ku yi idan haka ya shafe ku?

Saboda haka, FCC ta shawarci masu amfani da wayoyi da su tuntubi kamfanonin wayoyin hannunsu don neman karin bayani game da shirin su na dakatar da tsarin 3G.

Hakazalika, FCC ta bayyana cewa, tuni wasu kamfanonin suka fara sanar da kwastomominsu a shafukansu na intanet kan sauyin da za a samu, inda ta ce za a iya ziyartar tashoshin yanar gizon wayoyi domin samun karin bayani.

Kara karanta wannan

2022: Manyan biloniyoyi mata 10 na duniya, sunayensu, kasa da adadin dukiya

A bangare guda, an ce wasu wayoyin ba za su daina aiki ne kai tsaye ba, sai dai za su bukaci ingantayyar zubin na'urar sarrafa aiki.

Ga masu sayen wayoyi ba a hannun kamfani ba, ana shawartarsu da su duba cikin manhajar saitin wayar domin gano bayanai a cikin littafin kwastoma da wayar ke fitowa dashi don tantance tsarin sadarwar da ta fito dashi da kuma yiwuwar ingantayya.

Majalisar dattawa ta bayyana burinta kan sabis na 5G, ta ce NCC ta samar da N350bn

A wani labarin, Majalisar Dattawa ta nemi Hukumar Sadarwa ta Najeriya da ta yi amfani da tsarin sadarwa na 5G don samar wa Gwamnatin Tarayya kudin shiga N350bn a cikin kasafin kudi na shekarar 2022.

Idan baku manta ba, mun ruwaito muku cewa, gwamnatin tarayya ta amince a dasa tare da fara amfani tsarin sadarwar 5G a Najeriya, jaridar Punch ta ruwaito.

Wannan shi ne hukuncin kwamitocin hadin gwiwa na Majalisar Dattawa da ke aiki kan Tsarin Kudin Matsakaicin Shiri na 2022-2024, lokacin da gudanarwar Hukumar NCC ta bayyana a gaban kwamitin zauren majalisar.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Jami'in tsaro daya ya mutu yayin da sojoji suka ragargaji 'yan bindiga a Neja

Asali: Legit.ng

Online view pixel