2023: Zamu zabi kowace hanya da muke da ita wajen fitar da wanda zai gaji Buhari, Sanata Adamu

2023: Zamu zabi kowace hanya da muke da ita wajen fitar da wanda zai gaji Buhari, Sanata Adamu

  • Jam'iyya mai mulki ta ce ta shirya amfani da kowane ɗaya daga cikin zaɓi uku da doka ta tanada wajen zaɓen fidda gwani a 2023
  • Shugaban APC, Abdullahi Adamu, ya ce ba'a taɓa taro a tarihin zuwan mulkin demokaradiyya ba kamar na Maris
  • Ya ce ya kai wa shugaba Buhari ziyara ne domin gode masa bisa namijin kokarin da ya yi har APC ta yi nasara

Abuja - Jam'iyyar APC ta shirya amfani da kowane ɗaya ɗaga cikin hanyar kato bayan kato, Deleget, da Sulhu wajen fitar da ɗan takarar shugaɓan ƙasa a zaɓen 2023.

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta sanya wa'adin 3 ga watan Yuni kowace jam'iyyar siyasa ta gabatar mata da ɗan takararta, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Da yake jawabi ga manema labaran gidan gwamnati jim kaɗan bayan ganawa da shugaba Buhari, shugaban APC, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce jam'iyya mai mulki ta shirya wa kowane ɗaya ɗaga cikin zabi uku.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Na maida mutum 2,000 sun zama Attajirai a jihata, Gwamnan Arewa dake son gaje Buhari

Shugaban ƙasa Buhari da Abdullahi Adamu da Buni.
2023: Zamu zabi kowace hanya da muke da ita wajen fitar da wanda zai gaji Buhari, Sanata Adamu Hoto: Buhari Sallau/facebook
Asali: Facebook

Punch ta ruwaito Adamu ya ce:

"Idan lokaci ya yi zamu yi magana, hakan ya yi? Amma dai zabin na nan a ƙasa; zaɓen yan tinke, zaɓen Deleget da kuma hanyar Sulhu. Jam'iyya ke da ikon zaɓen wanne zata yi."

Ba'a taba taro irin wanda APC ta yi ba - Sanata Adamu

Game da babban gangamin taron APC da ya gudana ranar 26 ga watan Maris, 2022, wanda ya ayyana shi a matsayin ciyaman na ƙasa, Adamu ya ce:

"A tarihin demokaraɗiyya a Najeriya, tun daga jamhuriya ta farko ta biyu har zuwa yanzu, ba zan iya tuna wani taron ƙasa da ya kai wanda muka yi ba."
"Ba zan iya tuna babban taron da ake tsammanin ba zai yuwu a ƙare shi lafiya a sami nasara ba kamar wannan, muka gama lafiya kuma ina tunanin jagorancin da shugaban ƙasa ke samarwa APC ne yasa abun ya yiwu."

Kara karanta wannan

2023: Ba zan janye ba, waya sani ko yan Najeriya ni suke mutuwar son na gaji Buhari, Ɗan takara a PDP

Meyasa ya kai ziyara ga Buhari?

Sabon shugaban APC ya ce bayan shafe mako ɗaya a sabon Ofis ɗinsa, ya ga ya dace ya kai ziyarar godiya ga shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

"Tun bayan kammala taro a watan Maris, ba mu zo mun gana da shi ba domin mu gode masa bisa tsayuwar daka da ya yi aka sami nasara a taro."
"Yau muka samu da ma, shiyasa muka garzayo tare da tsohon shugaba, mu gode wa shugaban ƙasa da kuma sanar masa cewa an mika ragama."

A wani labarin kuma Gwamnatin Buhari ta bayyana abinda zata yi don ceto Fasinjojin Jirgin ƙasan Abuja-Kaduna

Gwamnatin tarayyan Najeriya ta tabbatar da cewa sai inda ƙarfinta ya ƙare wajen ceto mutane da yan ta'adda suka sace a Jirgin ƙasa.

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa ma'aikatarsa na aiki kafaɗa da kafaɗa da hukumomin tsaro don samun nasara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel